Bankin Manoma Ya Raba Bashin Naira Biliyan 895.5 A Jihar Kwara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Bankin Manoma Ya Raba Bashin Naira Biliyan 895.5 A Jihar Kwara

Published

on


Manajin Darakta kuma babban jami’I na Bankin Manoma na kasa (BoA) Kabir Adamu, ya sanar da cewa Bankin ya rabar da bashin naira miliyan 895.5 a jihar Kwara tun daga lokacin da aka kafa bankin a jihar, inda kuma ya koka yadda naira miliyan 227.4 ne kacal aka mayar daga bashin da aka bayar kuma gabaki dayan kudin naira miliyan  618.081m  har yanzu ba a maido da su ba ya kuma yi  kira ga wadanda suka karbi bashin, don wadanda basu amfana ba suma a basu.

Adamu ya bayyana hakan ne a lokacin da  Babban Darakta na sashen yan kasuwa dana ayyuka na Bankin dake Arewacin kasar nan  Mista  Emmanuel Ameh,ya wakilce shi a  taron bude sabon reshe na Bankin fake yankin Erin-Ile a cikin karamar hukumar Oyun dake cikin jihar.

A cewarsa, Bankin yana da rassa biyar a jihar wadanda duk suke a Ilorin, Lafiagi, Okuta, Iwo-Isin da kuma Erin-Ile ya kara da cewa, muna biyar da bashin yin aikin noma da kuma wanda bana yin noma ba kuma munada rassa 141  a daukacin fadin kasar nan mafi yawancinsu a karkara suke, inda mutanen karkara suke sukafi amfana.

Ya ce, Bankin yana karbar kudin ruwa tsakanin kashi 14 bisa dari akan bashin da ya bayar,inda ya ce sabon reshen Bankin da aka kaddmar zai bayar da bashi me a fannin aikin noma a karkashin sabon shirin.

Adamu ya kara da cewar, sabon shirin gwamnatin tarayya ce ta samar da shi wanda ya hadada samar da kudi , inda ya ce shirin ya taimaka wajen cimma Bankin burinsa akan tannin aikin noma da inganta rayuwar alumma.

Ya ce za a fara aiwatar da shirin ne akan mutane wadanda bashin da za a basu zai fara daga naira 20,000

A cewarsa, Bankin an kuma bashi dama wajen samar da kayan aikin noma don rage masu rashin aikinyi har ila yau ya ce, Bankin kuma ya kaddamar da shirin noma na Gwamnatin Tarayya na (Anchor  Borrowers).

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!