Janar Din Soja Ya Bace Makonni Kadan Bayan Ritayarsa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Janar Din Soja Ya Bace Makonni Kadan Bayan Ritayarsa

Published

on


Iyalan Manjo Janar Idris Alkali, mai ritaya sun sanar da bacewarsa makwanni kadan kafin barinsa aikin soja.

Matar janar Alkali, mai suna Salamatu Alkali, ta tabbatar wa da wata kafar yada labarai (DAILY NIGERIAN) cewa, ta daina jin duriyar mijin nata ne kimanin mako daya day a wuce a lokacin yana kan hanyarsa daga Abuja zuwa gonarsa dake jihar Bauchi.

“Kafin tafiyar tasa na shawarce shi da kada ya bi ta hanyar Jos saboda matsalolin dake tattare da hanyar, na bukaci ya bi ta hanyar Kano.

“Munyi maganar da dashi ta karshe a ranar da lamarin ya faru, in d ace mani sun wuce garin Jos, na sake yi masa korafin rashin bin hanyar kano, amma ya tabbatar mani da cewa, babu komai hanyar ta yi lafiya.” Inji matar a cikin alhinin rashin mijinta.

Ta kuma ci gaba da cewa, Rundunar Sojojin Nijerita ta bata tabbacin cewa, za su ci gaba da kokarin ganin sun ceto Janar din daga duk halin da yake ciki.

“Sun ce mu yi hakuri suna binciken wuraren da ake tsamanin za a iya ganiunsa, amma lallai hakurinmu na kara kurewa, kwanaki na kara wuce ba tare da wani labara ba, hankalinmu na kara tashi a kullum.

“Muna kira ga dukkan hukumomin dake da hannun a lamarin ceto shi das u kara kaimi don ganin sun dawo mana das hi cikin koshin lafiya.” Inji ta.

Duk kokarin jita bakin jami’in watsa labaran rundunar sojojin Nijeriya, Tedas Chukwu, ya ci tura don ya ki daukar wayar da ake yi masa bai kuma mayar da amsar sakon karta kwana da aka aika masa ba don matsayin rundunar sojojin a kan lamari.

Shi dai Janar Alkali, dan asalin garin Potiskum ta jihar Yobe, ya taba zama shugaban gudanarwa na rundunar sojojin Nieriya ya kuma taba zama mai rikon shugaban runduna 7 na sojojin Nijeriya.

Ya kuma taba tsira daga wani hari da aka kai musu da bam a lokacin yana aiki a cikin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ a garin Bama ta jihar Borno.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!