Karin Albashin Ma’aikata: Kungiyar Kwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Karin Albashin Ma’aikata: Kungiyar Kwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14

Published

on


Gamayyar Kungiyar ‘yan kwadago a Nijeriya tab a gwamnatin tarayya wa’adin kwana 14 wanda ya fara daga jiya dangane da tirka-tirkar albashi mafi karanci na ma’aikatan gwamnati.

‘Yan kwadagon sun zargi gwamnati da ministan kwadago da laifin dakile duk wata hanyar da za ta kai ga cimma nasarar batun karin albashin.

Dukkanin kungiyoyin kwadago guda uku da ake da su, a karkashin jagorancin shugaban kungiyar ‘yan kwadago ta kasa, Kwamared Ayuba Wabba sun gudanar da taron manema labarai jiya a Legas inda suka bayar da wannan wa’adi. Kungiyar ta ce, kwamitin da aka kafa don yayi bahasin albashi mafi karancin ya ki ya mika rahoton kwamitinsa ga Shugabansa, saboda bai aminta da mafi karancin albashin da aka yanke ba.

Wabba ya kara da cewa, gaza cimma matsayar adadin kudin da za a yi amfani da shi a matsayin mafi karancin albashi da gwamnati ta yi, ya nuna ba ta shirya yin aiki da batun ba kenan.

Ya ce, bayan da kwamitin da aka kafa ya kammala aikinsa sai ministan kwadago, Chris Ngige ya fadi wa kwamitin wai gwamnatin tarayya sai ta gudanar da tuntuba tukunna kafin ta aminta da adadin kudin da zai zama mafi karancin albashin. Wanda a cewarsa, hakan ya sabawa ka’idar da aka shimfida tun farko.

Ministan Kwadagon ya zargi gwamnonin jihohi da kawo tsaiko ga aikin kwamitin da aka kafa, amma shi kuma Shugaban Kungiyar Kwadagon ya musanta wannan zargi, inda ya ce, gwamnonin jihohi 21 tuni sun bayar da nasu bahasin ga kwamitin, inda da yawansu ma suka ce za su yi biyayya ga ko nawa aka yanke a matsayin mafi karancin albashin.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!