Ko Ka San Bambancin Ronaldo Da Messi? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Bambancin Ronaldo Da Messi?

Published

on


Tsohon dan wasan Manchester United da Manchester City, Carlos Tevez ya bayyana cewa abu guda daya ne kawai ya banbanta dan wasa Cristiano Ronaldo da takwaransa Messi saboda duka gaba dayansu ya buga wasa dasu.

Duka ‘yan wasannin dai su biyu sun lashe kofuna da kyaututtuka daban daban a rayuwarsu wanda hakan yasa har yanzu babu dan wasa kamarsu kuma suna cigaba da jan zarensu duk da cewa shekaru sun fara yimusu yawa.

Lokacin zaman Ronaldo a Manchester United da Real Madrid ya lashe kofin zakarun turai guda biyar da gasannin rukuni rukuni da kuma wasanni da dama sannan kuma  a haka yazama dan wasan da yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a tarihin Real Madrid.

Shima a daya bangaren, Messi, ya lashe kofin zakarun turai guda hudu da Barcelona sanann kuma ya lashe gasar laliga guda tara da ragowar kofunan da ya taimakawa kungiyar ta lashe sannan kuma shima shine dan wasan da yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a tarihin kungiyar.

Sannan kuma gaba dayansu kowanne acikinsu ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyar biyar wanda hakan yasa har yanzu ake tantamar wanda za’ace yafi wani acikinsu ta fuskar samun nasara da kwarewa.

Tevez yace tunda yake bai taba ganin Messi yana daukar horo shi kadai ba saboda duk abinda yakeyi kawai gani yayi ya iya amma ba koya yayi ba amma Ronaldo kullum yana filin daukar horo yana koyan abubuwa da dama.

Yaci gaba da cewa lokacin da suna Manchester United shi da Ronaldo idan an tashi daga daukar horon kungiya kullum sai Ronaldo ya tsaya yayi nasa da kansa kuma yafi kowanne dan wasa zuwa filin daukar horo akan lokaci.

“Idan akace za’a fara daukar horo karfe 9 to Ronaldo zaizo karfe 8 ko bakwai wataranar inason inga na rigashi zuwa da wuri amma duk irin sammakon da nayi sai naga ya rigani zuwa tun daga nan na sallama masa” in ji Tevez

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!