Connect with us

LABARAI

’Yan Son Rai: Kwankwaso Ya Mayar Wa Da Buhari Martani

Published

on

Tsohon gwamnan Jihar Kano, kuma mai hankoron ganin Jam’iyyar PDP ta tsayar da shi domin ya yi mata takarar shugabancin kasarnan, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya mayar da martani a kan zargin da Shugaba Buhari ya yi na cewa, duk wadanda suka fice daga Jam’iyyar APC raunana ne.

A sa’ilin da yake tarban wasu kungiyoyin sa kai ne a ranar Talata da suka saya masa Fom din tsayawa takara, Shugaba Buhari, ya kwatanta wadanda suka bar Jam’iyyar ta APC da ma’abota son rai kuma raunana a cikin Jam’iyyar.

Sai dai Kwankwaso, a cikin wata sanarwa ta hanyar mai taimaka masa kan harkokin manema labarai, Binta Spikin, cewa ya yi, “Kamata ya yi Shugaban kasan ya fito fili ya shaida mana ko da su wa yake yin wannan maganan.

“Amma dai shugabana da Rabi’u Kwankwason da na sani ba masu rauni ne ba, domin ayyukan ci gaban da ya wanzar sun isa su yi ma shi shaida.

“Ayyukan da ya iya yi a Kano, cikin shekaru hudu kadai, sun nu na irin karfin da yake da shi, shugaba ne shi mai hangen nesa, wanda ya san abin da yake da bukata da kuma hanyar da ya kamata ya bi domin ya same shi.

“Shi kadai ne shugaban da na san ya mayar da Kano bisa turban ci gaba, ya kuma aiwatar mata da manyan ayyukan raya kasa, fiye da guda 6000 a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015 kadai, har yanzun kuma suna nan, kowa na iya ganin su ya kuma iya taba su ma. Mutum mai rauni ba zai iya yin hakan ba.

“Hakanan ba zai zama mai son kai ba, saboda har zuwa yau shi ne kadai gwamnan da ba ruwan sa da karban kudadan tsaro. Kasantuwan kuma al’umma suna bin sa tamkar su bauta masa, hakan yana nu na karfin sa ne da kuma rashin son kansa, za kuma mu kai ga gaci.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!