Asalin Abin Da Ya Faru Na Kuskuren Saukar Jirgi A Abuja — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Asalin Abin Da Ya Faru Na Kuskuren Saukar Jirgi A Abuja

Published

on


A safiyar Jiya Alhamis ce, Matafiya da dama a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe suka kasance cirko-cirko bayan da wani jirgin sama na Gulfstream 4 mallakar Kamfanin Skybird ya kuskure hanayar sauka, inda hakan ya janyo tsaikon tashi da kuma saukar sauran jiragen sama a filin.

Lamarin ya auku ne da daren ranar Laraba.

Majiyarmu daga filin jirgin saman ta shaida wa wakilinmu cewa jirgin ya sauka ne a titin gudu na 22 inda aka ci sa’a ya tsaya a gefen ko-ta-kwana.

A cewar wata majiya da ba ta son a ambaci sunan ta, akwai tazarar mita 30 a tsakanin gefen ko-ta-kwana da karshen titin da jirgin ya sauka na 22, kuma iftila’in ya auku ne da misalin karfe  10.20 na daren ranar ta Laraba.

Har ila ayu, wata majiyar ita ma ta sheda wa wakilinmu cewar,  hanyar da jairagen ke tashi da sauka ya ji    ke sharkaf da ruwan sama wanda hakan ne ake tunanin ya sabbaba sabi-zarcen da jirgin ya yi.

Iftila’in ya janyo tsayawar tashi da saukar jirage a filin jirgin, inda hakan ya janyo matafiya suka kasance cirko-cirko a filin jirgin a ranar ta Alhamis.

Kakin yada labarai na hukumar filin jirgin Boke Ibbaze, ta sanar da cewar mahukuntan tashar jirgin suna sane da aukuwar lamarin.

Tuni dai Hukumar Kula da Zirga-zirgan Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) ta sanar da cigaba da sufurin jirage a filin jirgin bayan ta tabbatar da cewa komai ya daidaita.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!