Gwamna Badaru Ya Nemi Karin Kasafin Kudi Bilyan N29.3 A  2018 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamna Badaru Ya Nemi Karin Kasafin Kudi Bilyan N29.3 A  2018

Published

on


Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya nemi majalisar dokokin jihar Jigawa da amince masa da karin kasafin kudi na zunzurutun kudi har kimanin bilyan N29.324 a wannan shekara ta 2018.

Wannan kuduri na gwamnan na kunshe ne cikin wata takarda wadda shugaban majalisar ya gabatar gaban majalisar a jiya domin amincewarta.

Gwamnan ya bayyana cewa, wadannan karin kudade za\’a yi amfani dasu ne wajen gudanar da ayyukan raya kasa domin amfanin al’ummar jihar baki daya.

Ya ce, ayyukan wadanda suka hadarda ayyukan tituna, sanya wutar lantarki a kauyuka, bada tallafi ga mata da matasa, aikin samarda ruwan sha a wasu sassan biranen da wasu garuruwan jihar gamida sanya fitilun kan titi masu amfani da hasken rana.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!