Ina Arsene Wenger Ya Shiga? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ina Arsene Wenger Ya Shiga?

Published

on


A cikin watan Mayu ne dai Arsene Wenger ya ajiye aikinsa na kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal bayan ya shafe shekara 22 yana jagorantar kungiyar inda yasamu nasarori da dama a lokacin zamansa.

Bayan Wenger mai shekara 69 ya bar kungiyar Arsenal wadda ta sa ya yi fice a watan Mayun shekarar 2018, an yi ta rade-radi game da makomarsa inda wasu suke cewa zai koma kasar Sin wato China domin cigaba da koyarwa.

Rahotanni dai sun nuna cewa tsohon kocin Arsenal din yana amfani da damar hutun da ya samu wajen shakatawa da kuma cigaba da tattaunawa akan makomarsa bayan kungiyoyi da kasashe da dama sun neme shi.

A cikin watan Yuni an ga Mista Wenger ya shiga kwale-kwale da ‘yan uwa da abokan arziki a Cambridge dake kasar Ingila sai dai kuma duk da cewa mutane sun nemi daukar hoto da shi, Wenger bai nuna damuwa ba saboda abin da ya dame shi kawai shi ne yadda mai tuka jirgin kwale-kwalen ba zai fadi ba.

A lokacin da ake gasar kofin duniya, daga watan Yuni zuwa watan Yuli, Wenger ya yi aiki a matsayin mai fashin baki ga wasanni ga kafar nuna wasannin kwallon kafa ta beIN Sports.

A hirar da ya yi da wasu kafafan yada labari Wenger ya nuna cewa ba zai sauya sana’a ba sai dai kuma bai nuna inda zai koma ba amma bayan shakatawa da karance-karance, Wenger yana yawo kasashen duniya musamman Yammacin Afrika.

Ranar 24 ga watan Augusta ne tsohon dan wasan Wenger George Weah wanda a yanzu shine shugaban kasar Laberiya ne ya karrama Wenger da lamabar yabo mafi girma a kasar.

A ranar ne kuma tsohon shugaban kasar Ghana, John Agyekun Kufor, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar, dan kasar Faransan wato Wenger ya ziyarce shi a gidansa dake Ghana inda suka tattauna batutuwa da dama.

Fitattun ‘yan wasan da suka bar arsenal lokacin wenger

*Jens Lehmann: Ya bar Arsenal a 2008 ya koma kungiyar Stuttgart lokacin da kwantiraginsa ya kare a kungiyar daga baya ya yi ritaya. Ya sake komawa kwallo a shekara ta 2011 daga nan ya sake shiga Arsenal.

*Bacary Sagna: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Arsenal.

*Kolo Toure: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Arsenal.

*Thomas Bermaelen: A shekarar 2014 ya koma Barcelona daga Arsenal

*Ashley Cole: Ya koma buga wasa a Chelsea  ita kuwa Chelsea din ta bayar da William Gallas.

*Patrick Bieira: Ya koma wasa ne a Jubentus.

*Cesc Fabregas: A shekarar 2003 ya koma buga wasa a Barcelona.

*Marc Obermars: A shekarar 1997 ya koma Barcelona domin maye gurbin Luis Figo.

*Aledis Sanchez: Ya koma Old Trafford, inda Manchester United ta bayar da Henrikh Mkhitaryan.

*Robin ban Persie: A shekarar 2012 ya koma buga wasa a Manchester United.

*Thierry Henry: Ya koma buga wasa a Barcelona a shekarar 2000.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!