John Terry Ya Ki Amincewa Da Koma Sapartak Moscow — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

John Terry Ya Ki Amincewa Da Koma Sapartak Moscow

Published

on


Tsohon kaften din tawagar kwallon kafar Ingila wanda kuma ya taka leda a Chelsea, John Terry ya yi watsi da kwantiragin da kungiyar kwallon kafa ta Spartak Moscow ta Rasha ta yi masa tayi.

A cewar dan wasan, ya dauki matakin ne bayan nazari tare da iyalinsa kuma suka yanke shawarar cewa, a wannan lokaci ba za su iya barin in da suke ba don komawa Moscow.

Tun lokacin da kwantiraginsa ya kare da Aston Billa a farkon kakar da muke ciki, Terry  ke zama a gida ba tare da aikin buga kwallo ba sai dai rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea zata mayar dashi domin yashiga cikin masu taimakawa kociyan kungiyar.

Dan wasan ya buga wa Chelsea wasanni har sau 700 tare da taimaka mata lashe kofuna da dama da suka hada da kofunan firimiya guda biya da kofunan FA biyar da kuma gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2012.

Sannan kuma dan wasan ya bugawa kasar Ingila wasanni da dama ciki har da kofin nahiyar turai da kuma gasar cin kofin duniya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!