Yadda Muka Kwashe Da Iyayena Kan Kwallo Da Farko – Mane — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Yadda Muka Kwashe Da Iyayena Kan Kwallo Da Farko – Mane

Published

on


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Sadio Mane, ya bayyana cewa lokacin da yana matashi yana yawon neman buga kwallo iyayensa sunce dashi ya daina bata lokacinsa don zama babban dan kwallo gwanda yazama malamin makaranta.

Mane, wanda a yanzu haka yake daya daga cikin ‘yan wasan da babu kamarsu a kasar Ingila ko kuma a duniya ma gaba daya idan har ana maganar ‘yan wasan gaba ya ce sai da ya kulla yarjejeniya da babbar kungiya sannan iyayensa suka amince cewa zai iya buga kwallo.

Dan wasan mai shekara 26 a duniya ya bayyana cewa idan yana buga kwallo iyayensa da abokansa har dariya suke masa suna cewa gwanda yakoma yazama malamin makaranta kamar yadda ‘yan uwansa suke.

“Na girma a kauyen da babu wanda ya taba zama babban dan kwallo ya bugawa wata babar kungiya a duniya hakan yasa kowa yake cewa abinda nakeyi bamai dorewa bane gwanda in koma inyi karatu domin zama malamin makaranta” in ji Mane

Yaci gaba da cewa “Sai dai naci gaba da gayamusu cewa kwallon kafa itace hanya daya tilo da zan iya taimaka musu sai dai basu yarda ba saboda basuga wanda yataba zama babban dan kwallo ba gaba daya kauyenmu har sai da sukaga na samu kungiyar, sannan kuma tsakanin garinmu da babban birni da nisa sosai”

Mane dan kasar Senegal yakoma kungiyar Metz ta kasar Jamus kafin yakoma Red Bull Seilburg daga nan kuma sai yakoma kungiyar Southampton yanzu kuma yana Liberpool.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!