Connect with us

LABARAI

Yayin Da NEMA Ke Tantance Barnar Ambaliya A Kebbi, Mutum 10 Sun Sake Mutuwa A Adamawa

Published

on

Hukumar Bada agajin gaggawa ta gwamnatin taraiya ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan harakar ba da agajin gaggawa a jihar Kebbi tare da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar a jiya.

Shugaban tawagar, Dakta Onimode Bandele tare da shugaban yankin jahohin Kebbi, sakkwato da kuma Zamfara, Sulieman Muhammad wadanda ke wakiltar shugaban hukumar NEMA na Injiniya Mustapha Maihaja da kuma Daraktan sashen kula da bincike da kuma ba da kariya yayin gudanar da taron na masu ruwa da tsaki a jihar.

An gudanar da taron ne a dakin gudanar da taron na ofishin Mataimakin Gwamnan jihar ta Kebbi. Inda shugaban tawagar ya bayyana mukasudin kiran taron. Ya ce, “mun kiran taron masu ruwa da tsaki ne domin mu tantance adadin mutanen da suka rasa rayuwarsu, gonakin da ambiliyar ruwa ta illata da kuma adadin gidaje da ambaliyar ruwa ta lalata a cikin jihar ta Kebbi”.

Haka kuma ya cigaba da cewa “ za mu ziyarci kananan hukumomin da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar domin mu iya ganin illar da ambaliyar ruwa ta yiwa mutanen kananan hukumomin da abin ya da kuma shafa tattara bayanan abin muka gani domin basu tallafi na gaggawa”.

Ya kuma yi amfani da damar taron domin mika gaisuwar ta’aziyar shugaban hukumar ta NEMA ga gwamnatin jihar Kebbi da kuma iyalan marigayan da suka rasa rayuwar sanadiyar ambaliyar ruwa a jihar.

Shi ma da yake jawabin sa tun farko, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, Alhaji Sani Dododo ya bayyana damuwar hukumarsa kan irin yadda kananan hukumomi goma shatara cikin ashirin da daya da ke akwai a jihar ta Kebbi da  suka gamu da matsalar ambaliyar ruwa a yankunansu da  matsalar ta zama sanadiyar  lalata gidaje,  kayan amfanin gona kamar shinkafa, gore, masara,dawa da kuma arake da sauransu. Ya kuma cigaba da bayyanawa tawagar cewa “matsalar ambaliyar ruwa a jihar Kebbi tayi sanadiayar mutuwar mutane dayawa inda har da wani soja da yayi kokarin ceto wata mata ga rasa ranta sai shima ya rasa ransa sanadiyar yin agaji” .

Bugu da kari ya cewa” muna kan tattara sunayen wadanda matsalar ambaliyar ruwan ta shafa a dukkan kananan hukumomi goma shatara”. Har ilayau yace kananan hukumomin sun hada da Birnin-Kebbi, Kalgo, Bunza, Maiyama,Jega, KoKo-Besse da Bagudo.

Sauran kananan hukumomin sun hada da Gwandu, Dandi,Danko Wasagu, Zuru Fakai, Argungu, Yauri, Shanga, Arewa, Augie, Aliero, Ngaski da kuma Suru. Daga nan ya roki hukumar NEMA ta kasa da ta taimaka wurin gaggauta kawo agajin aggawa ga wadannan kananan hukumomin da abin ya shafa domin gwamnatin Kebbi ta yi iya kokarin ta na kokari na ba da tallafi ga wadannan mutanen, amma tallafin ba mai yawa ba ne.

A wani labarin kuma, Matsalar ambaliyar ruwa a jihar Adamawa, ta haifar da asaran rayuka mutane a kalla goma wasu da dama sun rasa gidajensu, sakamakon rushewar da sukayi.

Wannan bayanin na kunshe cikin wani bayanin da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ADSEMA ta fitar,  ta ce ambaliyar ya ci rayukan mutane akalla goma, mutane da dama sun zama ‘yan gudun hijira sakamakon wani mummunar ambaliya a jihar.

Dakta Muhammad Suleiman, shine sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da manema labarai a Yola, ya ce lamarin ya rusa gidajen jama’a da dama.

Shugaban ya ci gaba da cewa daruruwan dabbobin gida, da suka hada da Shanu duk an rasasu a ya’yin ambaliyar ruwa a jihar.

Ya ce “asaran rayukan da muka kididdige a kananan hukumomin Yola ta kudu, Guyuk,  Lamurde da kuma Song shine na mutane goma”.

“kuma ambaliyar ruwa na ci gaba da zamomana babban kalubale a Adamawa, yanayin kuma har yanzu na nuni da ruwan na kan zuwa.

“yanzu haka mutum 10 sun mutu, kuma daruruwan mutane sun rasa gidajensu, dabbobin gida adadi mai yawa aka rasa, sakamakon ambaliya.

“har yanzu manoma da dama, musamman a kananan hukumomi tara da suke yankin da kogin Binuwai ya ratsa, sun rasa kadada mai yawa koma gunakin gaba daya” inji Suleiman.

Ya kara da cewa ambaliyar ta hanfar da mummunan maishe da harkokin noma baya a jihar, lamarin da ya ce zai iya haifar da karancin abinci a jihar.

Dakta Muhammad Suleiman, ya ce akwai barazanar fiye da rabin adadin jama’ar jihar matsalar ambaliyar ka iya shafa, saboda haka ya nemi mazauna jihar da su kwanda sanin hakan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!