Real Madrid Ta Ware Fam Miliyan 330 Domin Siyan Manyan ‘Yan  Wasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Ware Fam Miliyan 330 Domin Siyan Manyan ‘Yan  Wasa

Published

on


Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tanada kudi kusan fam miliyan 330 domin kashewa akan sababbin ‘yan wasa ciki har da Neymar da Kylian Mbappe duka daga PSG.

Duka ‘yan wasan dai babu wanda ya fi su tsada a kasuwar siyan ‘yan wasa ta duniya bayan da PSG ta siyi Neymar kusan fam miliyan 200 daga Barcelona yayinda shi kuma Mbappe aka biya kusan fam miliyan 166 bayan ya bar kungiyarsa ta Monaco.

Tun bayan barin Ronaldo Real Madrid dai har yanzu kungiyar ba ta maye gurbinsa da wani babban dan kwallo ba duk da cewa kungiyar ta nemi dan wasan Chelsea Edin Hazard ba ta samu ba sannan kuma ta nemi Neymar shi ma ba ta samu ba.

Neymar dai ya zura kwallaye 32 cikin wasanni 35 da ya buga a kungiyar ta PSG yayin da shi kuma Mbappe ya zura kwallaye 25 cikin wasanni 47 da ya buga duk a kakar wasan da ta gabata da kuma wasannin farko na wannan kakar.

Real Madrid dai tana fatan maye gurbin Ronaldo da wani babban dan kwallo wanda duniya za tasan cewa ta siyi dan wasa mai tsada sai dai duka ‘yan wasan da kungiyar take nema za su yi wahalar siya duba da yanayin yadda kungiyoyinsu suke da kudi.

Sabon kociyan kungiyar dai ya fara buga wasanninsa na farko da kafar dama bayan sun samu nasara a wasanni ukun da suka buga kuma  a yau za su kai ziyara gidan kungiyar kwallon kafa ta Athletico Bilbao domin buga wasa na hudu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!