Connect with us

DAGA NA GABA

Barista Imamu Gazali: Gwarzonmu Na Mako Tarihinka

Published

on

Imamu Gazali Umar an haife ni a garin Bichi a shekarar 1978 na yi firamare a garin Bichi sannan na yi makarantar sakandire a makarantar koyon nazarin addinin muslunci mai zurfi  Higher Islamic da ke Shahuci daga nan na wuce jmi’ar Bayaro inda na karanci fannin  shari’a daga nan na wuce low school inda na zama cikakken lauya na yi bautar kasa a jahar Taraba.

 

Yaushe ka fara al’amuran siyasa?

To dai siyasa ba ta haife mu ba amma tare muka girma da ita.muna gani ana yi a makwabta kullum cikin al’amuran al’umma ake.  Na fara da rike shugaban matasa   Na shiga al’amuran siyasa kusan shekaru da biyar  zuwa talatin da suka wuce.muna cikin matasa a wanan lokacin. Wannan ya sa muka ga muna da wata gogewa ga kuma cudanya da da jama’a  ba ranar da za ta fito ta koma sai wani ya zo wajenka ko dai neman shawara ko neman taimako  Bayan rasuwar Gen Sani Abacha wadannan siyasu suka wuce  aka shigo da sababbin tsari na jam’iyyu a 1999 a lokacin mutanenmu da muka yi centre party daga nan muka shiga cikin jam’iyyar ANPP A wannan lokacin Allah bai ba wa team dinmu nasara ba sai muka zauna a kasa na dan lokaci. Mun yi gwamnati shekara takwas lokacin malam Ibrahim Shekarau. Yanayi ya haifar muka koma jam’iyyar ACN muka shiga zabe da maigidanmu Hon Ibrhim Mu’azzam Bichi  muka shiga zabe muka fadi daga nan sai jam’iyyar PDP suka nme mu mu zo mu tallafa musu su ci zabe. Muna nan a kwankwasiyya har lokacin da aka koma APC wanda muke ciki yanzu. Muna ciki mu rike alkawari muna tare da wannan gwamnatin mu da mutanenmu har Allah ya yi wa aigidan namu rasuwa. Bayan rasuwar maigidanmu Hon Ibrahim Mu’azzam Bichi sai wannan team ko gungun mutanen sai suka nuna suna da sha’awar kada wannan mutanen da ake tare su wargaje shi yasa suke ganin yana da kyau daga cikin mutanen da ake tare a samu wasu su fito takara. Ina cikin wadanda aka tuntuba a ciki akwai wanda ya nemi majalisar tarayya amma ni da yake ni ne karami sai na nemi majalisar jaha. A haka dai muke ta tafiya.

Na fara da rike siyasar dalibta lokacin ina jami’a na rike shugaban dukkan dalibai na karamar hukumar Bichi na kasa . A wannan lokacin duk inda dalibai suke na Bichi a jami’oi da kwalejoji da manyan makarantu na bi sun a kafa shuganci na jiha sama da ishirin local chapter. Kuma  na yi yi babban sakatare na na kungiyar dalibai masu karanta bangaren sharia. Lausa A lokacin ma da muka je Low school a Abuja nan ma mun yi shugabancin jami.oi 39 na yi sakatarensu Akw aai kungiyoyi da dama da ake cikinsu wanda duk manufofinsu tallafawa al’umma da gogewa a shugabancin al’umma. Alhamdulillahi wasu mutanen na wannan lokacin har yanzu ana tare da su a siyasance a yau. Suna kallonka a matsayin kai ka kama hannunsu ka ja su a siyasa.  na rike shugaban matasa na centre party a Bichi sannan bayan an kafa ja’iyyar APC na zama kakakin jam’iyyar ko sakataren yada labarai na jam’iyyar a karamar hukumar Bichi kuma mukamin daake rike da shi yanzu. Kusan kafin kafa jam’iyyar ma na

 

Kana a matsayin Lauya  kuma ka tsinci kanka a siyasa ya ka ke ganin al’amarin?

Kana tare da al’umma a koda yaushe safe rana da dare gidanka kullum kana tare da al’umma sannan ai shi lauya a kowanne lokaci a ko’ina ana nemansa a ko’ina har cikin gida ana neman lauya hatta shugaban kasa  da gwamna ba su da abokin shawara da ya wuce antony general domin bas a son su yi abin da ya kaucewa ka’ida don shi bay a son ya yi abin da ya aucewa ka’ida.Haka shi lauya kullum yak an zama mai tsawatarwa ne a cikin al’umma saboda ya san doka.

 

Ya ka ke kallon makomar matasa a siyasa yadda a yanzy suka yunkuro kan takarkari

To z aka ji ana cewa an danne matasa to amma ni ina kallon abin ne ta wata mahanga ta daban. Ko ‘yancin kai matasa ne suka karba kuma suka ci gaba da rike al’amura haka yake a yanzu duk da yake a yanzu duk da manyan na shiga to su ma matasan suna da nasu nakasun kamata ya yi su tashi su nemi makoma irin ta siyasa don suna da mutuwar zuciya irin ta siyasa z aka ga mutum ya kamata shi ma ya tsaya a takara ya sau amma sai ya koma yana tumasanci da jagaliya wanda wannan abun koma baya ne. amma bas u tsaya sanyin jiki ba don za ki ga matashi da yake da makoma a siyasa  kuma suna bayar da shawarwari na gari inda kuma in an bi su ana samun nasara. Amma akwai haske a cikin al’amuran matasa.

 

Ga shi a na ta darewa a jam’iyyarku ta APC.

Bari na yi miki gyara don ni ban yarda da wannan kalma ta darewa ba ita  siyasa ko kungiya kundin tsarin mulki ne ya bayar da dama dokar kasa ta ba wa kowa ikon  shiga duk inda yake so sai dai in yana sanye da wata riga wato wani matsayi a siyasa kamar sanata ko dan majalisa to yana da wani takunkumi idan zai fita daga jam’iyya to sai an sami tafarraka ko jam’iyyar ta rabu gida biyu sannan ne zai iya fita salin alin.Wadannan da suka fita har shugaban kasa ya yi musu ftan alheri  ai shugaban kasa daban sannan tsarin jam’iyya daban shi kansa shugaban kasa jam’iyyar APC ce ta zabe shi jam’iyya tana da damar ta bi Kadin hakan za ta iya.

 

To amma amma su ma ba sun yi R-APC ba?

Ai wannan ma sai an je kotu an tabbatar  idan ma kotu ta yanke hukuncin cewa it aba ta yarda da ma da function din  ba to suna ruwa ma’ana za a mayar da kujerunsu ba kowa ne sai dai a yi sabon zabe don cike guraben da suka fita

 

A siyasance wannan fitar da ake ta yi a jam’iyyarku ta APC ci gaba ne ko ci baya?

Ai duk dan siyasa ba ya son raguwa a tsari na rayuwa ma ba wanda yake son raguwa don haka raguwar wadannan mutane da aka samu a cikin jam’iyyar APC ba wani abu ba ne mai dadi.Ammaidan ka kalli siyasar Najeriya wadancan mutanen suna cikin gungun mutann da suka hana Buhari aiki wadansu mutane da suka yi masa tarnaki sun bar shi ni ina jin ma yanzu ne zai zauna da gindinsa don bas a tare da shi da duk sun hana ruwa gudu yanzu kuwa sun bar tsarin ruwan zai sheka a guje.

 

Me ne ka fahimta a siyasa?

I to kowa da  fahimtarsa amma ni fahimtar da na yi wa siyasa duk wanda Allah y aba wa dama a kowanne irin matsayi yana da nauyi guda uku. Na farko aikin da aka zabe shi don shi ya yi shi. Ya tabbatar yak are mutuncin wadanda suka zabe shi sannan  ya yi abin da ya tabbatar cewa zai gyara tsakaninsa da Allah.sannan ya gyara tsakaninsa da mutanen da suka zabe shi.Ya kare martabarsu a mu’amala sannan ya taimaka musu iyakar iyawarsa saboda shi da aka zabe shi ba a zabe shi ba ne don ya ji dadi shi da iyalansa ba su ma al’ummar da ke karkashinsa na son jin irin wannan dadin abin da Allah ya hore masa ya tallafa.

 

Ga shi kana neman kujerar dan majalisar jiha wane buri ka ke da shi ga al’ummar Bichi in Allah ya a ka?

Na farko wadancan abubuwa da na lissafa ta kansu zan fara su zan dabbaka sannan kuma na kara don kuwa mata na neman kulawa na musamman matsayinsu na iyaye da kuma tarbiyyartar da al’umma.Don haka ina da kudiri biyu kan mata na farko dai akwai wani abu da nake son yi pen for all inda zan bi lungu da sako in dai mace ce a Bichi da yardarm Allah sai ta iya karatu da rubutu wadanda suka bar makaranta za mu mayar da su mu dauki nauyin karatunsu komai da komai.Wadanda kuma muka fuskanci kwakwalwarsu da damarsu ba za su iya karatun ba za mu dauki nauyi nsu su koyi sana’a mu ba su jari da kayan aiki dai-dai gwargwado.

 

To ya ka ke ganin kamun ludayin gwaninka Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje?

Ai bayan zamansa gwanina kuma gwanin Kanawa ne don kuwa bayan gina al’umma ga ayyuka nan burjik bayan gadojin sama da kasa bayan tituna kalli aikin nan na lungu kyal-kyal ga wasu gine-gine a makarantunmu tun daga sakandire da firamare da ake yin wasu gine-gine hawa biyu sannan ga dakunan kwanan dalibai dubi ayyukan da aka yi a jamar Northwest da kuma wanda aka yi a jami’ar kimiyya ta wudil hannunsa ya zama kamar hannun gizo-gizo ba inda hannunsa bai kai ba. Hatta harkar samun ruwa da karasa  asibitin nan na Gidan zoo da Giginyu…

 

Amma kana lissafin wasu ayyuka da ban a Maigirma Dr Abdullahi Ganduje ne ba.

Ai nima cewa na yi ya karasa amma in ma dai adalci za a yi aikin da aka tsaya 30% ya zo ya yi 70% ai kamata ma ya yi y ace aikinsa ne yanzu mu yanzu misali jami’ar Northwest da ake magana ai zamanin mulkin soja aka yi kokarin farata da taimakon Mu’ammar Gaddafi amma yanzu w aka ji yana ambatarsa ina jin ko titi a ciki ba a yi tunanin saka sunansa ba.  Jami’ar Wudil lokacin Arc Kabiru Gaya aka fara ta amma yanzu w aka ji yana ambatarsa? Don haka ba laifi ba ne wani ya samar da abu wani kuma ya karasa.

 

Ana ta rade-radin gwamna Ganduje ba zai iya kawo kujerarsa saboda rabuwarsa da Kwankwaso.

Wanda yake ganin gwamna Ganduje ba zai kawo kujerarsa ba to imaninsa ya yi rauni don al’amarin kowa a hannun Allah yake. Mai girma gwamna mutum ne mai Imani cikakke ya san Allah ke bayarwa  kuma shi yake hanawa saboda haka mu a wajen Allah muke nema kuma da shi muka dogara. Bayan wannan maganar nan da ake cewa man jada wa jadda . Maigirma Gwamna shi ma ya yi iyakar nasa kokarin na ayyuka ki je Birni da kauye ki ga irin ayyukan da aka shimfida mutane na kallo  sannan kuma a siyasance  kamar ya hangi duk a a iya wannan rigimar don haka ya shirya don haka ya yi kokari ya samo mutanen da za su iya cike gurbi idan an sami baraka. Misali a karamar hukumata ta Bichi ya nemo tsohon dan jam’iyya Lawan shehu ya dawo da shi APC domin sum aye masa gurbin wanda za su tafi haka a Gwarzo ki je tsanyawa ki je tudun wada  saboda haka nasan Kanawa in ana zabe sai hudu ko fiye za su zabi Dr Umar Ganduje don ya yi kuma an gani.Farf agandar masu jarhula tuni an saba ji.

 

A na kallon Bichi kamar wata cibiya ko wani ruhi na siyasar Kano ya za a yi ku ci gaba da rike wannan kambun?

In sha Allah duba da yadda aka keto da gwagwarmayar da aka yi wannan lokaccinma muna nan daram kuma wannan kambun sai ma abin da za a sami ci gaba in har Bichi ta zo hannunmu. Za mu samar da sabon tunani don inganta jihar ba ki daya. Kirarin da ake yi wa Bichi na cibiyar Kano za mu rike kayanmu.Yanzu misali za a ce duk dan Bichi kada ya je aikin gwamnati to kuwa aikin gwamnati ba zai yi wu ba a ranar a jahar Kano.Karamar hukumar Bichi tana da rawar da take takawa don ci gaban Kano. Sannan a siyasance mutanen da suke cikin gwamnatin suna da tasiri kwarai a gwamnatin.Sannan in an zo wajen zabe ina da tabbacin Bichi ta Ganduje ce. In wasu suna wasu hange to daga nesa suke amma su je Bichin su gani .

 

Me ne Burinka?

Burina shi ne nag a an samar da al’umma ta gari kuma ta sami ci gaba . Mata su zama suna da ilimi wannan ya sa nake fatan a sami study centre a Bichi ta Open Unibersity wannan zai bayar da dama mata su sami damar ci gaba da karatu. Har ma mazan za su iya zuwa don ci gaba da karatu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!