Connect with us

NAZARI

Har Yanzu Ba Wanda A Ka Hukunta Da Laifin Kunna Wutar Rikici A Nijeriya?

Published

on

An jima ana rigingimu a Nijeriya tare da zubar da jinin bayin Allah saboda son zuciya, tun daga rikicin Biafra zuwa fadan zangon Kataf da yakin basasar Nijeriya zuwa rikicin Tafawa Balewa da na kala kato da na Boko Haram da sauran su. Abin da gwamnati ke yi bayan lafawar kowane rikici shine a kafa kwamiti a zauna a sha shayi a watse a kama wadanda basu da gata a tsare masu gata kuma idan rigima ta kwanta sai a sake su ta hanyar beli su gudu su bar kasar. Musamma a arewa ba a cika hukunta masu laifi ba, amma a kudu sukan dauki lauyoyi su jima suna fafata shari’a. Har zuwan wannan gwamnati ta Buhari an zaci za ta bayar da goyon baya wajen hukunta masu irin wannan kunna wutar rikici amma shiru ake ji sai yaki d cin hanci da rashawa da neman tara kudi.

Hakan ya sa har yanzu mutane na kunna irin wannan wuta gaban su gadi. Tun daga lokacin da aka fara rigimar Boko Haram a Nijeriya sanin kowane arewacin Nigeria an shiga cikin mawuyacin hali wanda a lokacin babu mai iya bayyana inda aka dosa sai ubangijin da ya halicce mu, musamman ganin yadda a wancan lokaci aka cusa gaba da kiyayya tsakanin kabilun arewa da kuma mabiya addinin musulunci da kiristan arewa.

Wannan lamari yana da ban mamaki musamman ganin yadda aka wayi gari kowa ke kulle da juna duk da kasancewar sanin kowanne ba wanda ya isa ya kori dan uwansa daga inda yake zaune. Allah ya hada zama waje guda babu wanda ya isa ya ce ga lokacin da za a rabu, kuma ko an rabu dole a ci gaba da begen juna musamman ganin yadda kowa ke Gadara da yankin da kowa ya fito a fannin tattalin arzikin da Nijeriya.

Yankin arewa ya fi shiga halin yaki da rashin tabbas wanda idan mutum ya wayi gari bai san me gobe zai taras ba saboda irin barazanar da zaman lafiyar yankin ke ciki musamman a wannan karni. Ba talaka ba har jami’an tsaro kan su na cikin mawuyacin hali saboda su da suke rike da makamai sun fi kowa sanin illar da makamai ke da shi, idan an kai hari an kashe jami’in tsaro zaka iske dan arewa ne ko wanda ya sha ruwan arewa. Haka kuma idan talaka aka kashe dan arewa ne idan ma’aikaci ne dan arewane yawanci, idan gine-ginen gwamnati ko na jama’a aka lalata arewa ne kuma kudin arewa za a kwasa a gyara, haka idan kasuwa aka kona ko aka durkusar da kasuwanci a gari duk arewa aka mayar baya, wannan ya haifar da matsananciyar wahala da talauci da rashin aikin yi da durkushewar lamurra a yankin arewacin Nigeria.

Abin tambaya a nan me yasa duk irin wannan bai cika faruwa a kudancin Nijeriya ba sai arewa? Ana nufin su basu da ‘yan ta’addar da za su iya aikata irin wannan aiki ne ko basa cikin talaucin da za su bukaci lada ko abin masarufin zaman gari daga irin abin da za su samu a sakamakon aikata wannan aiki na taaddanci ko basu da bukata ne? Abin mamaki a baya an wayi gari jami’in tsaro zai shiga gari a arewa ya kashe mutane ya fita abinsa ba abin da zai faru ya kar banza kamar yadda ya faru a kasuwar shanu ta Potiskum duk da irin jami’an tsaron soja da ‘yan sanda da aka jibge a garin wasu mutane dauke da bindigogi suka shiga kasuwar suka shafe sama da awa biyu suna bude wuta suka kashe maza da mata sama da mutane 200 suka kone kasuwar da dabbobi da dukiya wacce ba wanda ya san adadinta kuma har yau ba wanda aka kama kan wannan aiki .

Wannan ya sanya tababa a zukatan mutane inda suke gani a wancan lokacin akwai hadin bakin gwamnatin lokacin cikin lamarin. Bayan haka aka rika bi gida gida ana kashe duk wani mai fada a ji a garin na Potiskum da Borno da wassu sassa na Jihar Yobe, daga nan aka rika kame matasan gari Allah ya san adadin wadanda aka kama har yau babu labari an kashe wasu an raunata wasu kuma ba wanda aka hukunta har yau.

An wayi gari tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gamu da matsin lambar cewa bai taba ziyartar yankin Borno da Yobe ba duk da irin bala’in da suka fada a lokacin, don haka aka ja hankalinsa ya amince ya kai ziyara yankin, lamarin da ya sake jefa mutane cikin wahala inda a ka hanasu walwala duk da cewa a jirgi kurum ya yi ta yawo, amma a yayin da ya zauna da mutanen garin Maiduguri da nufin su bayyana masa kokensu game da cin zarafin da jami’an tsaro ke aikata musu kamar yadda a lokacin Farfesa Nuru Alkali ya wakilci jama’a ya yi jawabi tare da bayar da shawarar yadda za a samu mafita kan lamarin. Ashe sun kai kuka gidan mutuwa, saboda tashin shugaban kasa ke da wuya ya bayyana cewa ba za a a yi sulhu da ‘yan kungiyar Boko Haram ba saboda su fatalwane ba wanda ya sansu, to ina wadanda aka kama ake tsare da su a lokacin?

Don haka bayan tafiyarsa ked a wuya aka rika kama mutane ana harbewa, don haka idan da gaske gwamnatin shugaba Buhari tana da adalci kamar yadda ake mata zato ya kamata a binciki irin wannan tu’annati.

Tafiyarsa Goodluck ke da wuya a ranar juma’ar sai aka kai hari kan wata unguwar talakawa inda aka kashe mutane sama da dari aka ce an kama sama da saba’in tare da manyan makamai da bindigogi, lamarin da ke nuna masana harkar tsaro sun yi tababar gaskiyar labarin saboda ana ganin idan har ‘yan Boko Haram sun mallaki wadannan makamai  ba abin da zai hana su fitowa a fafata da su a lokacin ziyarar.

Lamarin bai tsaya a nan ba an ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kananan hukumomin arewa kamar yadda ya faru a Bama da Baga da Gujba da Gashua da Potiskum a Jihar Yobe da Mayo Belwa da Madagali a Jihar Adamawa da Wase da Ryom a Jihar Plateau da Ringim da Kano a Jihar Kano da wasu sassa na Jihohin Bauchi da Kaduna da Zamfara da Kebbi da Katsina da Wukari a Jihar Taraba da Gombe da Nassarawa da sauran sassan arewa da lokaci ba zai bari mu kirgosu ba. A kullum kai hari ake yi ana kashe ‘yan arewa da nakasa dukiyarsu amma an kasa daukar matakin da ya dace don kawo karshen lamarin kamar yadda masana irin su Dokta Datti Ahmed da Marigayi Sheikh Lemu da sauransu suka bayar da shawarar a nemi sabuwar hanyar magnce rikicin tun rai basu salwanta ba amma gwamnati ta ki amincewa a lokacin.

Amma daga baya an kafa kwamitin jeka na yi ka kan sulhu wanda bai hana komai ba daga abin da ya ke faruwa. Hakan na nuna matukar gwamnati na tura kudi a fannin tsaro zai yi wahala a kawo karshen wannan fitina saboda akwai masu cin arzikin rigimar suna arzuta kan su, kuma har yanzu haka lamarin ke faruwa. Don haka ya kamata a nemi masana kan harkar tsaro daga kowane fanni na rayuwa su ba da shawarar da ake gani za ta samar da mafita daga wannan masifa da ke addabar mutanen arewa a wancan lokaci, amma har yanzu ba wani batu kan nemo masu laifi da hukunta su.

Abin takaicine lamarin da ke faruwa a arewa, don ko su mayan arewa yanzu abin ya fi karfin tunanin su illa jamian tsaro da ke kokarin fafatawa da yan bindiga a kullum.  Ganin yadda hatta Sarkin Kano da shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari da su Sheikh Dahiru Bauchi da mutanen Izala a Jos da sauran su duk, basu tsiraba daga cikin irin wannan barazana haka ‘yan siyasar suma basu tsiraba jami’an tsaro basu tsiraba, an kai ga kowa an kuskure shi lokacin amma kwana ya kawo shi yanzu. A lokacin an kai wani matsayi da mutane suka fara fito na fito da ‘yan bindiga dadi kafin aka fara samun sauki.

An yi tunanin idan an kai wani matsayi kuma ana ganin masana ba abin da ya rage sai ‘yan kudu masu mulkin kasa a lokacin su fara maganar kiran taron raba kasa idan an yi dace kenan idan kuma ba a dace ba sai a ci gaba da yakar arewa sai duk wani gini da dukiya da rai mai amfani da ake Gadara da su sun lalace ko sun salwanta sai ace kowa yaje ya ci gashin kansa an raba kasa. Shike nan sai a bar arewa da matasa ba aikin yi da kasa babu arziki da kabilu ba hadin kai da mabiya addinin musulunci da kirista babu yarda da juna kamar yadda yanzu ake zaune a wasu kasashe na duniya cikin dardar. Fatar mu shine gwamnati ta mayar da hankali wajen hukunta masu jawo zubar da jinin bayin Allah kamar yadda ta ke mayar da hankali kan masu sace dukiyar bayin Allah da fatar Allah ya kawo mana karshen irin wadannan rigingimu ya tona asirin masu ci da jinin bayin Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!