Connect with us

WASANNI

Harry Kane Ya Fi Ronaldo A Yanzu – Erikson

Published

on

Kan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Christine Erikson, kan kasar Denmark, ya ce kan wasan gaba na kungiyarsu, Harry Kane ya fi Ronaldo na Jubentus saboda haka ba zai iya bayar da Kane a ba shi Ronaldo ba.

Kan wasan yaci gaba da cewa Ronaldo babban dan wasane kuma yaci kofuna da kyaututtuka da dama a duniya saboda haka bazaice karamin dan kwallo bane amma Kane yafishi a halin yanzu

Ya ce Ronaldo ya shiga sahun manyan ‘yan kwallo a duniya kuma yanada tarihin da manyan ‘yan wasa basu dashi har ila yau yanada tarihin da za’a dake ba’a karya ba amma duk da haka bazaice yafi Kane ba.

Sannan yace tsakanin  kane da Ronaldo duka manyan ‘yan wasane wakanda suke zura kwallaye a duniya a halin yanzu musamman yanzu da kane kin yake kan ganiyarsa bayan yazama wanda yafi kowanne kan wasa zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya.

Sai dai ya ce yana girmama Ronaldo saboda tarihin da yahada a matsayin sa na babban kan wasa kuma a manyan  kungiyoyi kamar Manchester United da Real Madrid..

Ya ce abu ne mai wahala a hada’ yan wasan guda biyu saboda kowanne acikinsu yanayin buga wasansa da ban kuma gasar da suke bugawa daban sannan kungiyoyinsu daban daban ne.

Erikson  dai yakoma Tottenham ne daga kungiyar kwallon kafa ta Ajak shekarun da suka gabata kuma yakasance kaya daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar a dai dai wannan lokaci.

Tun bayan komawarsa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dai har yanzu Ronaldo bai zura kwallo a raga ba bayan sun buga wasanni uku a gasar siriya A hakan yasa aka fara hasashen ko kan wasan zai iya buga abin azo agani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!