Connect with us

ADABI

Wakar ‘Kadaura’ Ta San Kano Marigayi Ado Bayero

Published

on

Fitaccen marubuci kuma marubucin wakoki da fina-finan Hausa Zahraddeen Nasir ne ya rubuta wakar ta Kadaura, wakar da ta ke ta ta’aziyya ce da kuma yabon gwani babba dan babba mai Martaba San Kano, Marigayi Alhaji Dr. Ado Bayero Allah ya haska makwancinsa ya jaddada rahamarsa gare shi Ameen.

Zahradden Nasir dai yana daya daga cikin shugabannin kungiyar marubutan Hausa ta Hausa Authors Forum (HAF) inda yake rike da mukamin Jami’in Yada Labarai na kungiyar, kuma PRO II a kungiyar Gamayyar Marubuta Wkokin Hausa da Manazarta ta Kasa reshen Jahar Kano. Zahraddeen Nasir shi ne marubucin littafin Sanadiyya. Ga dai wakar ta Kadaura daga alkalamin Zahraddeen Nasir, a sha karatu lafiya.

 

 1. Ba don ba a taba yi mana ba,

ba don tazo da sauri ba,

da don wannan dalilan ne da ba za muyi matta kuka ba.

 1. Idan na tuno da ranar nan,

ta shida ga watan shida din nan,

dubu biyu ce da sha-hudu ran juma’a ba zana manta ba.

 1. Ranar kuka da shassheka,

wasu tamkar ma su yo hauka,

in kai nazarin dalilansu dole kayi musu uzzuri babba.

 1. In da sanyi kayi rashin bargo,

ko kwa kayi rashin babban bango,

ya zaka ji ne cikin ranka? amsar ba zata zamo da sauki ba.

 1. Rabo da gwani asara ne,

maida tamka tai jidali ne,

rana ta rabo da gwarzonmu yaya ido ba zaiyi kwalla ba?

 1. Mutuwa mai sa tuno Allah,

mai sanya ayo zubar kwalla,

ita ce ta taho ta dauke sarki na kano namu adali babba.

 1. Dan Abdullahi Bayero,

mai kima tun yana yaro,

rasuwar fa dakayyi ka bar marayu da ba ma zasu kirgu ba.

 

 1. Sarki ne mai yawan baiwa,

ga shi da hannu na bayarwa,

a fagen hidima ga addini an masa shaida ba kadan ma ba.

 1. Masarauta tai kadaura ce,

inuwarta kwarai a yalwacce,

ta shigar kowa da kowa ce ba ta shigar kowa da kowa ba.

 1. Ka shigeta ka samu alfarma,

tuwon girma a tuka ma,

miyar nama a zubbo ma ga su ruwan sanyi ka kukkurba.

 1. A fagen hidima ga addini,

ya fita zakka cikin karni,

taimakon da ya yowa addini har abada ba za a manta ba.

 1. Ikonka Ilahu na roka,

kalami warka da na dauka,

zan zano rayuwar marigayi Mai-kano babba dan babba.

 1. Ka zuban hikima da fahimta,

a kalamaina Ka sa tsafta,

Ka ban fikira na fara na kare tsaf ban kuskure ma ba.

 1. Ashirin da biyar a lissafi,

a wata na bakwai mu dau tafi,

a Alif da dari tara da talatin yazo duniya baba.

 1. Baiwar da Ilahu Yai yi mar,

a yau ba wanda ya cim mar,

yawan ni’imar da Allahu Yai masa ba kowa ya yiwa ba.

 1. Farko dai dan sarauta ne,

kuma mai ilimin addini ne,

masani na tsaro da aiki na banki dan kasuwa gwani babba.

 1. Shekaru Allah Ya tara mai,

ashirin ita yai ta yin mai-mai,

hudu sau hudu har da karin guda hudu shin ko baku gane ba?

 1. Hudu sau hudu dai tamanin ce,

cikon hudu ko hudu din ce,

in kun hada shekarun duk tamanin da hudu ne kwarai baba.

 1. Matansa hudu a lissafi,

jikoki dari uku sunfi,

yawan zuri’a fa baiwa ce ba kowa Allah Yake ba ba.

 1. Yawan ‘ya’ya ni’imma ce,

Allah Ya ba shi yalwacce,

‘ya’ya sittin da guda biyu ba kowa anka baiwa ba.

 1. Yayo iliminsa ba shakka,

Kur’ani sai da yai sauka,

sannan yaje firamari kofar kudu ban digga aya ba.

 1. Sai ‘middle school’ ya fara can,

sunanta na da ada can-can,

Rumfa ta kwaleji yanzu ta koma don ba zan rufe muku ba.

 1. Ba kadai yaren bature ba,

ba ilimin zamani na ba,

har larabci ya koyo a S.A.S ba zamu manta ba.

 1. Gata bai sa ya zauna ba,

bai mike kafa a wofi ba,

aikinsa kawai ya fara a bankin Africa ba da sanya ba.

 1. Sannan N. A ya koma nan,

‘Natibe Authority’ kenan,

Matsayin mai-ga takarda yake aiki bai raina aikin ba.

 1. Ilimi baya yawa sam-sam,

ya nadde kafa ya koma ‘tam!’

koyon ilimi na mulki yaje baice gada ake yi ba.

 1. Wancan aikin da ya yi a da,

a N . A na magatakarda.

iliminsa yasa ya dawo ga yin aikin a matsayi babba.

 1. Majalissar nan ta dokoki,

ya wakilci Kano suna doki,

a Alif da dari tara har da hamsin da hudu shekaru uku ba.

 1. Doka ya zam wakilinta,

matsayin babba a tsarinta,

tamkar babban jami’in tsaro a Kanon yau in mu kai duba.

 1. Tafawa Balewa ya sanshi,

haka ne fa ya sa ya tura shi,

ya wakilci kasar sa Najeriya a kasar Senigal Jakada ba.

 1. Sha daya ga wata na ‘October’,

ya zamo sarkin Kano babba,

a Alif da dari tara ne da sittin da uku in mu kai duba.

 1. Shekaru hamsin yana mulki,

da daya kar kuyi mamaki,

a cikin daular Fulani ba ayi guda da yayo dadewar ba.

 1. Juma’a it a ce ta kawo shi,

Juma’a it a ce ta dauke shi,

ranar juma’a ya hau mulki kai! Baiwar nan ba kawai ne ba.

 1. Shekaru uku yau muna kewa,

ta rashin sarkinmu mai baiwa,

kai! Lallai maida gurbin gwani ba wai abu ne na sauki ba.

 1. Allahu cikin makwancin shi,

Ka sa haske kasa kamshi,

ranar tashi ka tasai cikin tawagar ManzonKa mai haiba.

 1. Allahu cikin wadatarka,

Ka iyo rahama ga bawanKa,

Kayi masa gurbi a  Aljanna ba don ni ba Ilahu na tuba.

 1. A riga ba a rashin nono,

a makera wuta a kan cinno,

don haka sarkin da anka zabo ba ayo zaben tumun dare ba.

 1. Sarkinmu Sunusi gwarzo ne,

domin jika ga sarki ne,

sirikin sarki magaji na sarki ba a kasa ya tsinta ba.

 1. Shekaru uku masu albarka,

da yayo mun gamsu ba shakka,

rokon da muke ga Allah Ya dafawa mulkinsa muc ci gaba.

 1. Baiti arba’in nayo dai-dai,

Zaharadden Nasir ni ne dai,

za na tsaya ne kawai a nan ba don abin cewa ya kare ba.

 

Alhamdulillahi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!