Connect with us

Uncategorized

Zan Kawo Cigaba A Karamar Hukumar Nassarawa, In Ji Hon Gawuna

Published

on

Daya daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC a karamar hukumar Nassarawa kuma wanda ya rike mukamai daban – daban, domin ci gaban wannan karamar hukumar, HON. MANSIR ISAH GAWUNA dai a boyayye bane idan a ka ambaci Dr. Nasiru yusuf Gawuna wanda ya bada gudunmuwa gagaruma a karamar hukumar Nassarawa, ta ayyukan raya kasa lungu da sako a wannan yankin karamar hukumar Nassarawa. Yankin karamar hukumar Nassarawa ma ta amfana da wannan jajirtaccen wanda ya gudanar da aiki ya gudanar da shugabancin karamar hukumar har karo na biyu. Wannan ne ya sa wasu kungiyoyi da kuma a’ummar yankin karamar hukumar Nassarawa suka bukaci Hon. Mansir Isah Gawuna da ya tsaya musu takarar dan majalisar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa. Ganin irin gudunmuwar da ya bayar a zamanin da suka rike karamar hukumar Nassarawa. Ganin haka ne ya sa wakilin, LEADERSHIP A YAU LAHADI, HARUNA AKARADA,  ya samu ganawa da shi domin jin ta bakinsa ko ya ya karbi wannan kiran al’ummar karamar hukumar Nassarawa? Ga dai yadda shirar tamu ta kasance:

Hon. Yaya ka karbi wannan kiraye – kiraye da akai maka domin ka karbi wakilci ‘yan karamar hukumar Nassarawa a majalisar jiha?

To muna godiya ga Allah wannan tambayawa taka gaskiyane an bukaci cin fito takara kamar yadda ka fada in wakilci al’umar karamar hukumar Nassarawa a majalisar kano. To gaskiyane yanzu kakar zabe ta kama kuma ‘yan takara da dama sun fito kuma suna bukatar tsayawa takara matakai daban – daban, ko kuma ince jam’iyyu suna ta kokarin fidda ‘yan takara. Bayan kiraye – kiraye daban ina da sha’awar fitowa takara na wakilci al’ummar karamar hukumar Nassarawa a majalisar dokoki ta jihar kano. Bayan binkice danai na yarda naga cewar zan bada gudun muwa a majalisar dokoki ta jihar mkano idan Allah ya yarda, Kuma in Allah ya taimakeni duk irin shawarwar warin da zamu nema a gurin masana da kuma masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Nassarawa jihar kano zamu iya kawo chanji fiye da wanda suke kan kujerar idan Allah ya taimakemu.

 

Ka na daya daga cikin wayanda suka goge akan harkar mulki tun ba yanzu ba. Domin kaine wanda ka dafawa Dr. Nasiru Yusuf gawuna a shugabancin karamar hukuma dayai har karo na biyu, kuma kazo ka zama sakataren mulki a wannan karamar hukuma lokacin Dr. Lamin Sani. Indai harkar mulkine ka riga ka sani, yaya zaka shawo kan matsalolin da suka addabi karamar hukumar Nassarawa idan Allah ya kai ga nufi yaya zaka shawo kan matsalolin?

To babbar nasara a harkar mulki itace ka zauna da al’ummar kasan menene matsalarsu. Ka tattauna da al’ummar a shawo kan matsala dakai dasu ba abinda kai kake so ba. Babban abin da muke kokari kuma muke data idan Allah ya yarda zamu tabbatar da cewa muna da wani majalasi da muke zama da masu ruwa da tsaki. Domin duk sanda wani abu ya taso idan muna so mukai kudiri a majalisa ko kuma gwamnati tazo dashi domin jin ra’ayinsu muga mun goyi bayan abin mu shigar da kudiri, domin ya zama don al’ummar mukayi badan tunanin kanmu ba. Bazamu iya amfani da tunanin kanmu ba domin ganin kawai haka mukaga ya dace muyi, wannan ba zamu taba yi ba in Allah ya yarda, sai abin da al’ummar sukace. Al’ummar da muka bi goyon bayansu suka zabemu sune zasu zama abokan shawararmu da tattauna abubuwanda ya kamata ayi. Kuma kamar yadda ka sani yana daya cikin dalilan da ya sa idan ka zama dan majalisa tun daga ta dattijai har izuwa ta kansila, gwamnati ke samar maka abubuwan da zakai yiwa mazabarka ayyuka, shi yasa ma idan Allah ya bamu nasara zamu zama mune na farko da zamu bude office a mazabunmu domin office ya zama shine wanda zamu rinka karbar korafe – korafe na al’umma. Domin wannan ofisoshin da zamu bude shine zai bamu kwarin gwiwa wajen isar da sako a majalisa.

 

To karamar hukumar Nassarawa karamar hukumace mai fadin gaske daga cikin kananan hukumomin Kano. Wasu guraren har yanzu basu jiyokanshin aikin wanda suka zaba ba a majalisa, wane mataki zaka dauka wajen gudanar da ayyuka a inda bai je ba idan Allah baka nasara.

To ai shine abinda nake gaya maka, idan kana zaune da al’umma idan kasan matsalar su kuma ka yarda su kake wakilta, to dolene ka ringa neman shawarwarinsu. To a irin wannanne zakai kokarin cewa ka kai wannan aiki yakai wajen, to a wannan karon idan Allah ya ida nufi to zasu ga bambamci. A baya kamar yadda ka fada munyi abinda ya shafi mulki, mazaba goma sha daya (11) ta karamar hukumar nassarwa babu inda hannunmu bai kai ba lokacin da kwamishinan gona yana chairman din karamar hukumar Nassarawa, zamanin da muka samu daman a gudanar da ayyuka kenan. Babban kalubalen da yake gabanmu yanzu bai wuce maganar harkar matasa harkar ilimi da harkar aikin ti da yadda za ‘ayi yaki da shaye – shaye da miyagun kwayoyi wanda zama dole mu hada kai da mazu ruwa da tsaki, mu waiwayi harkar matasa da mata muga yaya zamui mu samarwa mutane abubuwanda zasu samu sauki wajen gudanar da sana’oin yi, wadanda suke da sha’awar karatu muga wane irin taimako zamu yi musu muga cewar mun hada kai muga cewar harkar ilimi ta inganta a wannan karamar hukuma tamu, harkar aikin yi ta inganta sana’oin hannun sun samu, idan akai wannan to zai taimaki al’uma kai tsaye. Maganar aikin mazabu kuwa akai ayyuka wadanda ba zasu irgu ba wanda gwamtin jiha take yarda suyi, said an majalisa yaje ya shiga ya fita kana a jarje masa yaje yayi aikin da yake so yayiwa mazabarsa. Inka wuce nan akwai ta gwamtin tarayya, akwai dan majalisa na tarayya wanda shi kuma dan wannan karamar hukuma ne, shima zamu hada kai dashi muga abubuwan da ake samowa a gwamtin tarayya itama karamar hukumar nassarawa ta samu, domin idan Allah ya bamu nasara nasarace ta ‘yan karamar hukumar Nassarawa baki daya. Ya zama dole duk wani abinda muka san zai kawo gyara domin ci gaban ‘yan karamar hukumarmu dolene mu shiga mu yi shi.

 

Ganin ‘yan takararnan gashi kuna da yawa, yaya kake ganin zaka bullowa abin idan Allah ya bawa wani zaka bishi.

To kamar yadda ka fada duk sanda akace akwai bukata ta siyasa in akace lokaci yayi duk wanda yake ganin munzalin ya cancanta dole zai fito. Kuma fitowar ‘yan takara da yawa ba abinda zai tsoratamu kuma idan Allah ya bamu mun gode masa haka muke so kuma idan mun samu akasin haka ma to mun godewa Allah, to amma dai Allah muke gayawa domin dai yasan manufarmu ta alheri ce domin mu kawo ci gaba a wannan karamar hukuma tamu. Don haka Allah ta’ala zai mana kuma zamu nasara akan duk abubuwanda muka sa a gaba. Kamar yadda muka bada gudunmuwa a karamar hukuma, to yanzu muna so Allah ya kaimu majalisar dokoki ta jihar kano domin mu bada gudunmuwa kamar yadda muka bayar baya.

 

Wasu idan suka je majalisa sai ace basa komai basa isar da sakon wanda suka zabesu a majalisa, wane mataki zaka dauka domin kore wancan zargi da akewa wasu ‘yan majalisa da zarar sun hau?

To ai rashin sanin abinda zakayi da rashin sanin tuntubar mutanenka shine yake sa wasu basu yin komai a majalisa. Amma indai ka yarda kana cikin al’ummar kuma al’umma sun bujiro da abinda suke so kuma wannan abin suke so shine matsalarsu kuma kaima shine abinda ya dameka, zancen kaje baka kawo wani kudiri a jalisa bama ai bai taso ba. Bama cikin wanda za’a samemu da wannan matsalar, kuma muna rokon Allah kada Allah yabar da iyawar mu da tunaninmu, Allah ya bamu iko muga al’umma sun amfani damar da mukaje da ita majalisa.

 

To Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana so ya maimata karo na biyu a wannan jiha, wane kokari kukeyi domin ganin cewa yakai gaci?

To idan kadai Dr. Abdullahi Umar Ganduje kadimul islam mai girma zababben gwamnan jihar kano wanda muna kyautata zaton zai zama gwamnan jihar kano a kakar zabe mai zuwa kamar yadda muke cewa 4 + 4. Mu kamar a karamar hukumar Nassarawa inda nafi sani nafi wayo, idan kace a lussafa ayyukan Dr. Abdullahi umar ganduje da yayi to an hada ka da aiki. Tun daga kan hanyoyi makarantu kai duk wani abu da ka sani tun daga lungu kal – kal, abubuwa da dama wanda mai girma wanda wasu da suke ganin mai girma gwamna kamar dan karamar hukumar Nassarawa ne. to amma saboda rashim kyakykyawan wakilci wanda zasu fito suyi bayanin ayyukan mai girma gwamna abun nema yakeyi ya gagara. Bana zaton akwai wani gwamna daya gabatar da ayyuka kamar yadda mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi a karamar hukumar Nassarawa. Domin idan aka fito aka tallata aikin mai girma gwamna to jam’iyyar zata samu saukin cin zabe tare dashi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!