Bana Son A Dinga Hadani Da Iniesta, Cewar Coutinho — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Bana Son A Dinga Hadani Da Iniesta, Cewar Coutinho

Published

on


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Phillipe Coutinho ya bayyana cewa bayason mutane su dinga hadashi da tsohon dan wasan kungiyar, Andries Iniesta wanda ya bugawa kungiyar wasanni da dama.

Iniesta ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona 674 tun lokacin da ya fara buga wa kungiyar wasa sannan ya lashe kofuna da dama a rayuwarsa ciki har da kofin duniya daya lashe a shekara ta 2010 wanda aka buga a kasar Africa ta kudu.

Coutinho dai ya koma Barcelona daga kungiyar Liberpool a watan Janairun wannan shekarar akan kudi fam miliyan 142 inda ya zura kwallaye 11 cikin wasanni 27 daya buga wa kungiyar sannan ya lashe kofin laliga da na Copa Del Rey.

Sai dai duk da ya fara buga wasa a kungiyar da kafar dama Coutinho ya bayyana cewa baya son a dinga hadashi da tsohon babban dan wasan kungiyar saboda dan wasa ne wanda bashi dana biyu kuma ya sadaukar da rayuwarsa a kungiyar.

“Iniesta dan wasa ne na daban wanda kungiyar nan za ta dade bata yi dan wasa kamarsa ba kuma bana son a dinga hadani dashi saboda babban dan wasane kuma nima ina son in kafa kaina in zama ana yin kwatance dani” in ji Coutinho

Ya ci gaba da cewa yana so ya ci gaba da buga wasa mai kyau kuma ya kasance duk inda aka sakashi zai yi kokari saboda shi ma yana son ya ci gaba da kafa tarihi kamar yadda kowanne babban dan kwallo ya kafa a rayuwarsa.

Coutinho dai kawo yanzu ya zura kwallo daya sannan ya taimaka an zura kwallo daya cikin wasanni biyar daya buga a kungiyar ta Barcelona a wannan kakar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai