Wakilin Ozil Ya Mayar Wa Da ‘Yan Wasan Jamus Martani Mai Zafi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Wakilin Ozil Ya Mayar Wa Da ‘Yan Wasan Jamus Martani Mai Zafi

Published

on


Wakilin dan wasan kasar Jamus kuma dan wasan Arsenal, Mesut Ozil ya mayar wa da ‘yan wasan kasar Jamus da suka hada da Tony Kroos da Thomas Muller da Manuel Nuer martini bisa sukar dan wasa Ozil da suka yi bayan ya yi ritaya daga buga wa kasar  Jamus wasa.

Ozil dai yaja hanaklin duniya bayan daya bayyana cewa ya daina bugawa tawagar ‘yan wasan kasar Jamus din wasa sakamakon zargin da ya yi na cewa hukumar kwallon kafar kasar bata goyi bayansa ba lokacin da wasu daga cikin ‘yan kasar suka zargeshi akan ya yi hoto da shugaban kasar Turkiyya.

A watannin baya ne dai aka hango Ozil da dan wasa Ilkay Gundogan na Manchester City sun yi hoto da shugaban Turkiyya Erdogan a birnin Landan din kasar Ingila abin da ya ja su ka daga bangarori da daman a kasar ta Jamus sakamakon rashin jituwa da take tsakanin kasar Jamus da Turkiyya.

‘Yan wasan kasar ta Jamus da suka hada da Tony Kroos na Real Madrid da Thomas Muller na Bayern Munchen da kuma mai tsaron ragar kasar Jamus shi ma dan kungiyar Munich din sun zargi Ozil da halin rashin girmama kasarsa da kuma rashin zuciya.

Sai dai wakilin dan wasa Ozil, Erkut Sogut, ya bayyana cewa ‘yan wasan basu yiwa Ozil adalci ba bisa zarge zargen da suka yi masa na cewa baya kishin kasar Jamus sannan kuma suka kirashi da dan wasa mara zuciya.

“Basuyiwa dan wasa na adalci ba saboda ya sadaukar da rayuwarsa ga kungiyar tawagar Jamus na tsawon shekaru amma bai kamata su gaya masa maganganun da suka ga dama ba kawai saboda ya yi ritaya saboda wasu dalilai” in ji wakilin dan wasan.

Ya ci gaba da cewa “Dole sai Tony Kroos ya fito yayi wa duniya bayanin dalilin daya sa ya ce Ozil ba shi da zuciya a kan kawai ya daina bugawa Jamus wasa sannan suma ragowar ‘yan wasan kasar dole su fito su kare kansu”

Advertisement
Click to comment

labarai