Daga Littafin Amanna (14) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

DAGA NA GABA

Daga Littafin Amanna (14)

Published

on


Amatullah ta harari mijinta “tun jiya ya ki ya fada mana ma abinda ya tsare shi da har ya kama shi ya kwana a waje, tunda nake da kai shekaru goma sha biyu baka taba kwana a wani waje ba alhali kana garin baka yi tafiya ba.”

Iziddin ya sunkuyar da kai kasa bai yi magana ba.

Nauwara ta sharce hawaye cikin sheshshekar kuka ta ce “yanzu haka kaina ke ta ciwo ina kyautata zaton jinina ne ya hau.”

Iziddin ya yi dariya ya ce “ zo in auna in gani ko jinin ne ya hau da gaske.”

Haushi ya kama su kowaccensu ta tashi ta shige bangarenta a fusace.

Khamis ya gyara zama ya dubi Iziddin wanda ke kishingide ya rufe idanuwansa da hannunsa kamar mai gyangyadi  ya ce “ ina ka je ka kwana ne?” Iziddin ya yi shiru bai ba shi amsa ba.

Khamis ya sake gyara zama ya duba gabas da yamma kudu da arewa ya tabbatar babu kowa a falon sannnan ya yi Magana cikin rada “ko neman Zahidah ne ya kai ka da nisa har ka bace hanya?”

Iziddin ya dago da sauri ya dubi Khamis duba na takaici.

Khamis ya yi murmushi ya ce “ka kwantar da hankalinka dan Allah abokina, an riga an tabbatar mana  Zahidah tana raye, kuma na fada na maimaita zaka sha mamaki.”

Iziddin ya yi ajiyar zuciya ya maimaita “Mamaki? Wannan wanne mamaki ne da har yanzu ban sha shi ba Khamis? Tun ba yau ba kake fadar haka duk sanda zan dauko maganar Zahidah sai ka fadi wannan Kalmar, har yanzu banga abin mamakin ba kuma. Sai yaushe ne?”

Khamis ya yi murmushi ya ce “ka ci gaba da hakuri dai. Amma dan Allah ka daina haka kada ka sake yiwa matanka haka, ka san suna sonka da yawa duk motsin da ka yi suna begenka ba kamar ni ba wanda matata bata damu da ni ba. Akwai Maganata da kai akan gimbiyata sai mun hadu a ofis zamu yi.”

Iziddin ya hasala ya dube shi duba na rashin fahimta “wacce gimbiyar?” Khamis ma ya harare shi ya tuntsire da dariya “au baka ma san gimbiyata ba ma zaka ce? Wai kai babban yaya ko? To Izzatunka nake nufi kasan saura kwanaki goma sha biyar ta gama iddah bana son in wuce karshen wata ba’ayi magana mai karfi ba.”

Iziddin ya mayar da kai ya kwanta bai bashi amsa ba.

Khamis ya mike tsaye yana murmushi ya ce bari in koma ofis kasan MD ya dawo ko? Kai ma naga alama kwana kayi baka yi barci, ba baka da niyyar fita ma yanzu bari in tafi idan ka kimtsa ka fito. Ka canje ni yau kai ka zama mai gyangyadi dan har suna ka saka min mai gyangyadi a ofis.”

Takaici ya hana Iziddin ya bashi amsa ya fada a ransa “tabbas yanzu na gano bakin zaren na gane a club kake kwana shiyasa aiki yake gagararraka da safe.”

Iziddin ya mike tsaye ya mikawa Khamis hannu ya ce “toh na gode sai anjima.”

Khamis ya fice da sauri ya yin da Iziddin ya nufi bangarensa yana tafe yana tangadi kamar zai fadi. Muryar Amatullah ya ji ta ambaci sunansa

“Abban Faruk.”

Ya juyo da sauri ya dube ta, ta karaso in da ya ke, sai ta nuna masa teburin cin abinci  ta ce “ba daki za ka shiga ba abinci za ka ci saboda girkin Nauwara ne jiya ta sha wuyar yi maka girki baka dawo ba, yau da sassafe ta shiga kicin ta hada maka ba zata ji dadi ba idan baka ci ba.”

Ya mike kai tsaye ya nufi kan tebur ya zauna, Amanatullah ta shiga bangaren Nauwara ta kira ta suka fito tare. Bayan Nauwara ta zuzzuba musu sai suka zauna suka yi bismillah suka fara ci babu abinda suke yi sai kallonsa ci yake kamar baya so, dakyar yake hadiya. Daga ya ajiye cokali sai ya ci karo da guru- gurun idanuwansu sai ya yi sauri ya tura lauma bakinsa, kamar wani yaro karami. Nauwara ta yi ajiyar zuciya ta ce “me yake damunka ne wai?”

Ya sunkuyar da kai kasa bai amsa mata ba.

Ta sake cewa “a ina ka kwana ka canja kayan jikinka? Ina shaddar da ka fita da ita jiya?”

 

Advertisement
Click to comment

labarai