Watakila A Sake Hukunta Ronaldo Da Karin Wasanni Uku — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Watakila A Sake Hukunta Ronaldo Da Karin Wasanni Uku

Published

on


Rahotanni sun bayyana cewa watakila hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai, Eufa, ta sake dakatar da dan wasa Ronaldo karin wasanni uku, idan har aka same shi da laifin rashin da’a.

Christiano Ronaldo ya fice daga filin wasa cikin hawaye bayan alkalin wasa ya manna masa jan kati, yayin fafatawar Jubentus da Balencia a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a ranar Larabar da ta gabata.

Alkalin wasan dan asalin Jamus, Felid Brych ya kori Ronaldo ne a minti na 29 da  fara wasa a Estadio Mestalla, bayan ya yi cacar-baka da Jeison Murillo da ke tsaron bayan Balencia.

Murillo na bibiyar Ronaldo sau da kafa a wasan har ta kai ga gwarzon dan wasan ya kai masa duka a yayin da suke gwagwarmayar daukar kwallo.

Nan take Murillo ya fadi kasa, lamarin da ya ja hankalin alakalin wasa har ya gana da mataimakinsa kafin daga bisani ya dawo cikin fili don nuna jan kati ga Ronaldo.

Yanzu haka dan wasan ba zai buga wasan da Jubentus za ta yi a ranar 2 ga watan Oktoba ba da Young Boys a matakin rukuninsu, sannan kuma ana ganin ba zai buga wasan da Jubentus din za ta kai ziyara Old Trafford ba, domin buga wasa da Manchester United.

Idan har kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafar turan ya zauna ya tabbatar da Ronaldo ya nuna halin rashin da’a za’a iya karamasa wasanni uku akan hukuncin hakan yana nufin ba zai buga wasannin da za su fafata da tsohuwar kungiyarsa ba gida da waje da kuma wasan da Jubentus za ta buga da Young Boys a ranar 2 ga wata.

Advertisement
Click to comment

labarai