Zaben 2019: Gwamnoni Uku Za Su Kada Gwamna Daya A Kano – Kabiru Gaya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Gwamnoni Uku Za Su Kada Gwamna Daya A Kano – Kabiru Gaya

Published

on


Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Mazabar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa ta Kasa, Sanata Kabiru Gaya ya bayyana cewa zaben 2019 da ke tafe za a fafata ne a tsakanin Gwamnoni uku da kuma Gwamna daya a gefe guda inda ya ce ukun za su rinjayi daya.

Ya bayyana hakan ne a cikin tattaunawarsu da wakilin LEADERSHIP A YAU Juma’a, a gidansa da ke Unguwar Wuse 2 a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Sanata Gaya ya nunar da cewa komawar Malam Ibrahim Shekarau APC ya sa an samu hadin kan Gwamnoni uku a gefe daya tare da bayyana cewa wannan alheri ne ga al’ummar Kano. “Shigowar Malama Ibrahim Shekarau jam’iyyar APC alheri ne, kuma za ka dauki misali mai sauki, karamin lissafi shi ne, Gwamnoni hudu ne a Kano, guda uku tsofaffi, guda daya kuma mai ci. In ka dauka za ka ga Ganduje shi ne Gwamna mai ci, hekarau tsohon Gwamna ne, in ka dauko Kabiru Gaya tsohon Gwamna ne kuma Sanata mai ci a kan kujera. To ka ga nan mu uku muna bangare daya, wanda yake daya bangaren tsohon gwamna ne kuma Sanata mai ci, to in Allah ya so ukun ce za ta kayar da daya”.

Da aka tambaye shi ko yaya yake kallon yadda zaben shekarar 2019 zai kasance ta fuskar tsaro? Sai ya ce, “ In Allah ya so za a yi zabe lafiya, kuma Shugaba Buhari zai ci kujerarsa ta Nijeriya in Allah ya yarda, mu ma a Kano Ganduje zai ci zabensa, ni ma Sanatocin mu guda uku da ‘yan majalisar tarayyarmu na Kano duk in sha Allahu za su ci zabensu.

“Haka kuma a Nijeriya muna fatan APC za ta samu mafi rinjaye a majalisa da sauran wurare, saboda haka muna ganin in Allah ya yarda muna da wannan nasarar, kuma za mu gina al’umma aka cigabn wannan kasar. Abin da ya sa nake cewa Buhari ya sake maimaitawa abu biyu ne, na farko ina da kwarewar na yi Gwamna, kuma ko Gwamna, ko Shugaban kasa, ko Shugaban karamar hukuma, idan ka zabe shi, to shekara daya da rabi ta farko yana tunanin ya zai tafiyar da gwanatin ne kawai, ba zai yi wani abu mai kwari ba. Shekara ta biyu ko zuwa uku a nan ne zai fara aiki, amma shekara uku zuwa hudu, ba abin da zai maka kamfen zai tsaya ya yi na neman takarar ya koma.

“To ka ga a cikin mulkinsa na shekara hudu, ya samu aikin shekara biyu kawai, wanda Nijeriya za ta amfana, amma in mutum ya maimaita zai shekara hudu ga biyu, ka ga ya yi shekara shida a cikin shekara takwas. Wannan cigaban Nijeriya ce, cigaban jiha ne, cigaban karamar hukuma ne. Shi ya sa lokacin da Shekarau yake neman Gwamna karo na biyu aka ce wai ba a yin Gwamna biyu a Kano, na tsaya na taimaka masa da sauran mutane, ya yi hawa na biyu, aikin da ya yi a hawansa na biyu ya fi aikin da ya yi a hawa na daya. Haka Kwankwaso da ya hau mulki a shekarar farko ta hudu, aikin da ya yi a shekara hudu ta farko, bai kai aikin da ya yi a shekara hudu ta biyu ba. To kullum ka zo ka samu mai mulki zai shekara takwas, in dai mai mulki abin kirki yake yi, to za a amfana fiye da yadda ake tsammani. Don haka Alhamdulillahi, muna fatan jama’a su zo su sake zabar mu, kamr yadda mu ka yi Sanata sau daya sau biyu sau uku, yadda muke majalisa na tabbata ilimin da muka samu zai taimaka da yawa”, in ji shi.

Da aka tambaye shi ko mene ne ra’ayinsa a kan ‘yan siyasa masu sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata? Ya ce, “ To mutane suna mantawa, shekaru hudu da suka wuce, duk lokacin da zabe ya zo na siyasa, za ka ga cewa mutane suna canja sheka dai-dai yadda za su iya zama, mutane suna komawa jam’iyyar da za ta yi musu alfarma, mutane suna komawa jam’iyyar da suke ganin za ta iya cin zabe, ko kuma suna komawa jam’iyyar da za a hada kai da su a ci zabe.

“Misali wadansu sun fita sun tafi PDP, amma wadanda suka dawo mana APC har yanzu a Sanatoci mu ne muke da mafi rinjaye, a majalisar Dattawa ma mu ne da mafi rinjaye. Ka ga cewa kenan wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari in sha Allahu za ta zama alheri, kuma za mu yi nasara in Allah ya so ya yarda. Saboda haka wannan canje-canje ba wata matsala ba ce.”

“Akwai wasu da suka sauya wata shekar suna tsammanin lokacin da Buhari ya ci zabe, zai kyale su su yi handama da babakere da ruf da ciki, to sai suka gwamnatin Buharin nan ba ta barin a yi sata, ba bababkere babu handama, kuma ana sa su a gaba zuwa kotu. To ganin wannan wasu suka ce to bari su bar wannan sheka su koma wata, to ga ani lokaci an koro ka daga wani wuri, an ce abinda ya koro bera daga wani wuri ya fada wuta, to ya fi wutar zafi,” kamar yadda ya bayyana.

Kazalika Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya yi tsokaci irin nasarorin da yake ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a shekaru uku da ya yi a kujerar mulki, wanda ya ce, hakan wata manuniya ce da ke isharar samun nasara a zaben da ake fuskanta na shekarar 2019.

Wato Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ayyuka  da ba za su misultu ba, yanzu idan ka dauki hanyar da ta shi daga Bidda Lamba ta wuce zuwa Neja kenan, ita ma yanzu an bayar da kwangilar ana yin aikin. Ka ga wannan zai taimaka wa duk masu manyan motoci daga motar ma ice, maotar tank ice da sauransu. Wannan aiki duk zai ba da ikon cigaba bin wadannan hanyoyi, wato motocinmu na Arewa da suke bi.

Idan ka dauko daga hanyar Kano, ka taho Zariya, ka zo Kaduna, har zuwa Abuja, tun lokacin Shugaba Babangida aka gina hanyara nan ba a taba yi mata ko faci ba, shekarar PDP 16 tana mulki, amma yanzu da Allah ya kawo Shugaba Buhari a samu aikin nan an ba wa wani babban kamfani yana aikin nan.

Idan ka dauka yanzu daga Abuja zuwa Nasarawa, har Keffi, har ka shiga Benuwe, duk wadannan hanyoyi an ba da kwangila ana yin su. Idan ka dauka daga Kano zuwa Maiduguri, an ba da aikin nan tukuru ana yi, idan ka dauka daga Kwanar Dangora Kano kenan, har zuwa Tudun wada, har ka shiga Saminaka ana aikin nan, in ka dauka daga Kano zuwa Katsina gyara ne shi ma ana yi By Pass ta Kano ana yi. Sannan tun daga Sokoto ka dawo zuwa Zamfara, har ka zo Zariya ana yin aikin nan, to ka ga Shugaban kasa ya yi ayyuka da yawa a kan hanyoyi. Kuma Alhamdulillahi sai mu gode masa.

Advertisement
Click to comment

labarai