Ko Ka San Sau Nawa Aka Ba Wa Cristiano Ronaldo Jan Kati? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Sau Nawa Aka Ba Wa Cristiano Ronaldo Jan Kati?

Published

on


Wani abu daya saka shakku a zukatan masu kallon kwallon kafa a wannan satin shine yadd alkalin wasa Felix Bryd ya bawa dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo jan kati a wasan da kungiyar Juventus ta lallasa kungiyar Valencia daci biyu babu ko daya a wasan gasar cin kofin zakarun turai a ranar Laraba.

Wannan mataki da alkalin wasa ya dauka na korar dan wasan yasa dan wasan yafita daga cikin fili yana kuka sabida jan katin wanda yake ganin kamar bai kamata alkalin wasan yayi masa wannan hukuncin ba.

Sai dai wasu da dama suna ganin kamar hukuncin da alkalin wasan ya yanke akan Ronaldo yayi daidai saboda kafin yabashi katin sai da yaje ya tambayi mataimakin alkalin wasa suka tattauna sannan suka yanke hukuncin korar Ronaldo daga filin.

Mutane da dama dai suna ganin kamar hukuncin da alkalin wasan yayiwa Ronaldo yayi tsauri duba da girman dan wasan da kuma ganin cewa baya yawan aikata laifi irin wannan a fili kuma yawanci alkalan wasa suna duba halayen dan wasa kafin su bashi jan kati.

Ronaldo dai yabar filin wasan cike da hawaye a fuskarsa wanda hakan yake nuna damuwa da nadamar abinda yafaru kuma tuni masana masu sharhi akan wasanni suka fara sharhi akan ko ya cancanta alkalin wasan yabawa Ronaldo ko kuma bai cancanta ba.

Wasu suna ganin nasarar da dan wasan yake da ita a nahiyar turai da gasar gaba daya ya kamata alkalin wasan ya dagawa Ronaldo kafa duba da yadda dan wasan ya buga wasanni 154 batare da anbashi jan kati ba sai a wannan satin.

Bayan an bawa dan wasan jan kati ne kuma wasu rahotanni suka bayyana cewa hukumar ta nahiyar turai zata iya karawa dan wasan adadin wasannin da bazai buga ba idan har aka duba akaga laifin yakai a koreshi daga filin

Amma kuma rahotanni sun bayyana cewa watakila hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai bazata sake dakatar da dan wasan  ba Cristiano Ronaldo daga buga wasanni uku wanda hakan wani labari ne mai dadi ga dan wasan da kuma kungiyarsa ta Juventus.

Sai dai Ronaldo dole bazai buga wasan da kungiyarsa zata buga na gaba ba da kungiyar Young Boys kamar yadda doka take ga duk dan wasan da aka bawa jan kati amma zai iya buga wasan da Juventus zata buga da tsohuwar kungiyarsa Manchester United.

Da farko dai anyi tunanin hukumar kwallon ta nahiyar turai zata sake duba katin korar da aka bawa Ronaldo da niyar idan aka tabbatar yayi abin da ganganne za’a sake bashi karin wasanni biyu.

Sai dai hukumar kula da kwallon ta nahiyar turai zata yanke hukunci a ranar Alhamis mai zuwa inda zata bayyana matsayinta akan jan katin tare da la’akari da rahoton da alkalin wasa Felix Bryd, dan kasar Holland zai kai akan abinda yafaru.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Rio Ferdinand, ya bayyana cewa tababs alkalin wasa yayi kuskure wajen bawa Ronaldo jan kati saboda bai cancanta da abashi jan katin ba duba da halayayyarsa mai kyau a fili.

“Bai kamata a bashi jan kati kai tsaye ba kuma a farkon wasa saboda girman wasan da kuma yanayin dadan wasan yake ciki na cike da kalubale tun bayan barinsa kungiyar Real Madrid” in ji Ferdinand.

Shima takwaransa na Manchester United, Gary Nebille, ya bayyana cewa yakamata hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai ta duba yanayin da ake ciki kuma bai kamata ba hukumar har tayi tunanin zata kara masa wasu wasannin.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Juventus, Maximiliano Allegri ya bayyana cewa cin fuska ne ga Ronaldo a bashi irin wannan jan kati a gasa kamar ta zakarun turai kuma bayan laifin da yayi bai kamata ayi masa hakaba.

Sau Nawa Aka Ba Wa Ronaldo Jan Kati A Duniya?

Tun lokacin da Ronaldo yafara buga wasa a babbar kungiya ta sporting Lisbon da kuma zuwansa Manchester United da Real Madrid kawo yanzu a Juventus an bawa Ronaldo jan kati guda goma a tarihi kuma wannan wanda aka bashi a wasan Juventus shine na goman amma wasu suna ganin guda tara ne saboda wanda aka bashi na farko a rayuwarsa daga baya an soke katin gargadin da aka bashi na farko tunda daman katin gargadi biyu aka bashi kafin jan katin.

A lissafe dai an bawa Ronaldo jan  kati guda hudu a Manchester United sai kuma guda hudu a Real Madrid yayinda kuma aka bashi na farko a Juventus kuma shine na takwas a lissafin da a ke yi.

An bawa Ronaldo jan katinsa na farko a ranar 15 ga watan Mayu na shekara ta 2004 lokacin da yana buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a wasan karshe na gasar firimiya a shekarar a wasan da Manchester United ta doke kungiyar Aston Billa daci 2-0 har gida.

Sai dai daga baya an soke masa jan katin sakamakon korafin da akayi na cewa katin gargadi na farko da aka bawa dan wasan bai cancanta ba kuma hukumar FA ta Ingila ta soke shi haka yaci gaba da buga wasa a sabuwar kakar wasa batare da an dakatar dashi ba.

Sannan an bashi jan kati na biyu a ranar 14 ga Watan Janairu na shekara ta 2006 lokacin da ya doke tsohon dan wasan Manchester United, Andy Cole, a wasan hamayya da aka buga tsakanin Manchester City da Manchester United wasan da United din tasha kashi daci 3-1

Sai kuma jan katinsa na uku da aka bashi a ranar 15 ga watan Agusta na shekara ta 2007 lokacin da yayi amfani da kansa yayiwa dan wasan kungiyar Pothmouth gware mai suna Richard Hughes a wasan da aka tashi 1-1 a filin wasa na Fratton Park dake kasar Ingila.

An bawa Ronaldo jan katinsa na hudu ne kuma a wasan da Manchester United ta doke Manchester City har gida daci 1-0 a rabar 30 ga watan Nuwamba na shekara ta 2008 inda alkalin wasa ya bawa Ronaldo jan kati bayan ya doki dan wasa Shawn Right-Phillips sannan kuma aka bugo wata kwallo a yadi na 18 din Manchester City ya saka mata hannu alkalin wasa Howard Webb yabashi jan kati.

Bayan yakoma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma Ronaldo yasamu jan katinsa na farko ne a wasan da Real Madrid ta doke kungiyar Almeria daci 4-2 a ranar 5 ga watan Disamba na shekara ta 2009 wato shekarar daya koma Real Madrid kuma a wasan yaciwa Real Madrid kwallonta ta hudu sai dai ya zubar da bugun fanareti.

A ranar 24 ga watan Janairu na shekara ta 2010 Ronaldo ya karbi jan katinsa na shida bayan ya doki dan wasan tsakiya na Malaga Patric Mtiliga bayan ya dokeshi da gwuiwar hannunsa sai dai kuma Ronaldo ne ya zurawa Real Madrid kwallayenta guda biyu data samu nasara tun a farkon wasan.

Ranar 17 ga watan Mayu na shekara ta 2013 rana ce mafi muni inda abokiyar hamayyar Real Madrid wato Atletico Madrid taje har gida ta doke Real Madrid a wasan karshe na cin kofin Copa Del Rey kuma sai da Atletico Madrid tayi shekara 14 bata samu nasara akan Real Madrid ba sai a wannan rana kuma aka bawa Ronaldo jan kati.

An dakatar da Ronaldo wasanni uku a ranar 2 ga watan Febrairun shekara ta 2014 bayan an bashi jan kati kai tsaye a wasan da Real Madrid ta buga 1-1 da kungiyar Athletico Bilbao bayan da Ronaldo yayi sa’insa da dan wasan baya na kungiyar wato Carlos Gurpegi.

Sai kuma laifi mafi muni da Ronaldo yayi aka bashi jan kati a wasan Real Madrid da Cordoba a gasar Laliga bayan ya mari dan wasan baya na kungiyar Edimar a wasan da Real Madrid tasamu nasara daci 2-1.

Sai jan kati na karshe kuma na tara da Ronaldo ya karba a wasan da aka buga tsakanin Real Madrid da Barcelona wasan da Ronaldo yaci kwallo ya cire riga alkalin wasa yabashi katin gargadi tunda daman doka ce dan wasa yacire riga ana cikin fili,

Sai kuma bayan anci gaba da wasa ya fadi acikin yadi na 18 na kungiyar Barcelona yanason alkalin wasa yabashi bugun fanareti sai dai alkalin wasan yace Ronaldo sharri yayi kuma yabashi katin gargadi na biyu sannan kuma yabashi jan kati.

Wannan shine jumallar jan kati goma da Ronaldo yasamu a tarihin rayuwarsa daga Sporting Lisbon zuwa Manchester United da Real Madrid sai kuma wanda aka bashi a wannan satin a wasan daya bugawa Juventus da Balencia.

Sai dai wani abin mamaki har yanzu ba’a bawa Ronaldo jan kati ba a wasannin daya bugawa kasarsa ta haihuwa wato Portugal kuma duk da irin wasannin daya bugawa kasar.

Gaba daya jan katin da aka bashi a tarihi guda hudu daga ciki duk sai bayan an bashi katin gargadi guda biyu yayinda yasamu biyu a gasar firimiyar Ingila lokacin da yake Manchester United sai kuma daya a gasar Laliga sai kuma guda daya a gasar Super Cup

Sai kuma jan kati wanda aka bashi kai tsaye guda 7 biyu a gasar firimiyar Ingila sai guda uku a gasar laliga sai kuma daya a Copa Del Rey yayinda dayan kuma na karshe shine wanda aka bashi a satin daya gabata.

‘Yan Wasan Da Su Ka Fi Samun Jan Kati A Duniya:

Binnie jones – Ingila (jan kati guda 12)

Felipe Melo – Brazil (jan kati guda 14)

Yannick Cahuzac  France (jan kati guda 17)

Pablo Alfaro sipaniya (jan kati guda 18)

Paolo Montero Uruguay (jan kati guda 21)

Aledis Ruano Delgado sipaniya (jan kati guda 22)

Sergio Ramos sipaniya (jan kati guda 24)

Cryil Rool  Jamaica (jan kati guda 27 )

Gerardo Bedoya Colombia (jan kati guda 46)

 

Advertisement
Click to comment

labarai