Mun Yi Daidai Sayar Da Ronaldo, Cewar Real Madrid — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Mun Yi Daidai Sayar Da Ronaldo, Cewar Real Madrid

Published

on


Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya bayyana cewa matakin da kungiyar ta dauka na siyar da Ronaldo mataki ne mai kyau kuma sunyi dai-dai duk da cewa magoya bayan kungiyar basuji dadi ba.

Ronaldo dai yakafa tarihi a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tun bayan komawarsa kungiyar daga kungiyar Manchester United a shekara ta 2009 inda ya zura kwallaye 450 cikin wasanni 438 daya buga a kungiyar.

Sai dai a kakar wasan data gabata dan wasan ya gama bugawa kungiyar wasa bayan ya kammala komawa kungiyar Jubentus dake kasar Italiya akan kudi fam miliyan 105 bayan kammala gasar cin kofin duniya.

“Cinikin dayafi kowanne tsada a duniya a wannan shekarar shine na Ronaldo kuma bamu siyar dashi ba sai da mukayi tunanin sosai mukaga idan muka siyar da dan wasan bazamu samu matsala ba” in ji shugaban kungiyar

Ya ci gaba da cewa “Ronaldo ya gaya mana cewa yanason barin kungiyar saboda haka bazamu iya hanashi tafiya ba dole muka hakura muka tattauna da kungiyar da zata iya biyan abinda muke bukata akansa”

Tun bayan komawarsa Juventus dai Ronaldo kwallaye biyu kacal yaci kuma sai da yabuga wasanni uku batare daya zura kwallo ba sannan kuma a satin daya gabata aka bashi jan kati a wasan cin kofin zakarun turai a wasan da kungiyar ta buga da Valencia.

Advertisement
Click to comment

labarai