An Kammala Tantance ’Yan Takarar Majalisu Na  PDP A Kano — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Kammala Tantance ’Yan Takarar Majalisu Na  PDP A Kano

Published

on


A wannan Asabar ne ta jiya da ta gabata aka kamala Tantance masu neman zama Yan Majalisu a matakai daban daban a Jam’iyyar PDP bangaran Kwankwasiyya karkashin jagorancin shugaban PDP bangaran Kwankwaso Injiniya Honorabul Sulaiman Bichi da mataimakinsa Honorabul Dan Kaka Husainin Bebeji wanda aka gabatar a Birnin Kano.

An dai tantance Yan Majalisu a matakan Sanatoci dana Majalisar wakilai sai kuma na Jahohi duk da wasu basu samu yarjewa na samun Fom din ba da akace tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata Kano ta tsakiya Injiniya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya saye Fom din Yan Takarar baki daya na Kano.

Daga cikin wadanda suka bayyana gamsuwarsu da wannan Tantancewa a kwai Honorabul Sani Aliyu Rano mai gidan Bulo Dan Mjalisar wakilai mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure wanda yace shi dan asalin Kibiya ne da aka Haifa a Garin Kibiya, Hon. Zaharaddini Kabiru Gwadabe daga Danbatta, Hon. Ambasada Bala Aboki mai neman Da Majalisar Jaha a Nasarawa, Dr. Salim Dala, Hon. Zare Rogo mai neman Dan Majalisar Jaha a karamar Hukumar Rogo.

Shi kumwa Hon. Salisu Hamisu Kore ya bayyana damuwarsa ne akan yadda shi bai samu Takardar Izinin tsayawa takarar ba daga karamar Hukuma Tudunwada da dai sauran wadanda aka tantance a wannan rana.

Sai dai kuma wakilinmu ya rawaito mana cewa PDP a Kano na fuskantar matsaloli masu yawa musamman da ake ganin ta dare gida biyu a Kano inda akwai bangaran PDP Kwankwasiyya karkashin Sanata Jagoranci Sanata Kwankwaso da kuma bangaran Ambasada Aminu Bashir wali wanda ya kunshi shugabancin Sanata Masa’ud Doguwa da kuma Sanata Bello Hayatu Gwarzo a matsayin gidan da ya hada shugabanni uku a bangaran Jagorancin shugaban PDP Sanata Doguwa kamar yadda Alhaji Yahaya Bagoburi ya bayyana cewa tafiyarsu su uku ne wannan gida.

Advertisement
Click to comment

labarai