Idan Obasanjo Na Da Matasala Da Ni Wannan Matsalarsa Ce –Atiku — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Idan Obasanjo Na Da Matasala Da Ni Wannan Matsalarsa Ce –Atiku

Published

on


Ranar Asabar din da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa, ba shi da matsala da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Atikun wanda yana daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar, PDP ya bayyana hakan ne ga kwamitin jam’iyyar na jhar Nasarawa tare da wakilai masu zabe a tattaunawar da suka yi da shi a garin Lafiya, babban birnin jihar ta Nasarawa.

Lokacin da aka bukaci ya yi bayani kan sabanin da ke tsakaninsa da tsohon mai gidan nasa, Atikun sai ya ce, shi ba shi da wata matsala da tsohon shugaban kasar.

“Ba ni da wata tsala tsakanina da tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo, amma shi idan yana da matsala da ni wannan kuma matsalarsa ce” in ji Atiku.

Haka kuma ya yi alkawarin zai bunkasa tattalin arzikin Nijerya matukar ya samu nasara a zaben shekara ta 2019.

Kamar yadda ya ce, rashin tsaro da talauci da yunwa na daga cikin abubuwan da suka dakile ci gaban kasar nan.

Haka kuma ya ce, ba daidai ba ne a ce wai matasan Nijeriya ci-ma-zaune ne, wadanda bas u san wahala su nemi kudi.Kamar yadda ya ce akwai bayanai da dama da suka nuna irin kwazon da matasan Nijeriya ke da shi, haka ma manya maza da mata kullun suna kokarin neman hanyoyin da za su dogara da kansu. Saboda haka ya ce matukar an zabe shi zai kara samar da hanyoyin da za su karfafa gwiwar ‘yan Nijeriya na tabbatar

Advertisement
Click to comment

labarai