Ko Ka San Abin Da Ronaldo Ya Gaya Wa Alkalin Wasa Bayan An Bashi Jan Kati? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Abin Da Ronaldo Ya Gaya Wa Alkalin Wasa Bayan An Bashi Jan Kati?

Published

on


Gaba daya idon kowa ya koma kan tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo don aga wace uwa zai tsinanawa sabuwar kungiyar tasa ta Jubentus a wasansa na farko a gasar zakarun nahiyar Turai, amma sai dai abin mamaki shi ne yadda aka ba shi katin rashin da’a kai tsaye a mintuna na 29 da fara wasa.

Sai dai da yawan mutane basu gano mai ya faru ba sai bayan da suka yi karo da Jeison Murillo sai dai  daga baya dai an gano cewa ashe Ronaldo ya ja gashin dan wasan ne wanda kuma mataimakin alkalin wasa ya gani.

Kuma a dalilin hakan ne kuma aka bashi jan kati kai tsaye don haka dole ya fice daga filin wasa kamar yadda akayi a ranar Larabar data gabata.

Kafin ficewarsa daga filin an hango shi yana magana da alkalin wasan domin ya shaida masa cewa bai aikata komai ba ko zai canza hukuncin da zai dauka akansa sai dai tuni alkalin wasa ya yanke hukunci.

Na’urar hoto ta hasko shi yana cewa “Ban yi komai ba” amma hakan a banza, sai da aka aike da shi wajen fili kuma a karshe Jubentus din ce tasamu nasara a wasan daci 2-0 a wasan farko na rukuni

Wannan jan kati dai shi ne irinsa na farko da aka taba bawa Ronalso a wasanni 154 da ya buga a gasar zakarun nahiyar Turai, wanda hakan ke nufin cewa ba zai buga wasan da zasu buga da Young Boys ba a wata mai zuwa.

Advertisement
Click to comment

labarai