Mutane Biyar Sun Mutu A Hatsarin Mota — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Mutane Biyar Sun Mutu A Hatsarin Mota

Published

on


Mutum biyar ne suka rasa ransu a wani hatsari da motoci uku suka yi a kan babbar hanyar Birninkudu zuwa Kano a karamar hukumar Birninkudu da ke jihar Jigawa.

A jiya Lahadi 23 ga watan Satumba 2018 ne hatsarin ya afku a wani waje da ake kira Kwanar Gangare dake karamar hukumar Birninkudu.

Jami’in ‘yan sanda mai magana da yawon hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, sannan ya tabbatar da mutuwar mutum biyar a sanadiyyar haduwa da masu motoci uku suka yi da junansu.

Advertisement
Click to comment

labarai