Matasan APC Suna Goyon Bayan Silas Agara A Gwamnan -Kungiyar Matasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Matasan APC Suna Goyon Bayan Silas Agara A Gwamnan -Kungiyar Matasa

Published

on


A ranar Juma’a ne dandazon matasa maza da mata suka gabatar da gangamin nuna goyon baya ga dan takarar gwamnan Jihar karkashin inuwar APC Honarabul Silas Ali Agara a garin Lafiya. Matasan sun zaga manyan tituna a cikin garin Lafiya dauke da kwalaye da hutunan dan takarar suna rera wakokin nuna goyon bayansu gare shi.

Inda sukaya da zango a ofishin niman zaben Silas Agara dake kan titin Jos a Bukan  Sidi cikin garin Lafia.

Da yake karanta jawabin Matasan Jagoransu Mista Adeh Abubakar ya ce; mu matasa mana nuna goyon baya ga Dan takarar gwamna Honarable Silas Agara saboda ya cancanta yasan mahimmanci Ma’aikata da alumman Jihar Nasarawa.

Ya ce, zaben Agara cigaban Jihar Nasarawa ne. Ya nuna ana samun daidaituwa a bangaren siyasa . ya ce; Agara tare yake da gwamna Al-makura ya san yadda ya gabatar da ayyukan ci gaba a Jihar, kuma ta nan shi ma zai kama.

Ya ce; maza da mata al’umman jihar Nasarawa suna yaba wa da yadda dan takarar ke tafiyar da ayyukan hadin kan jihar Nasarawa.

Kungiyoyin da suka kasance cikin wanan gangamin ta nuna goyon bayan Silas Agara sun hada (NAYEF) (BISAA) (AAF) (NGM) (NANS). Sun yi

Sun yi kira ga masu zaben fidda gwani ta Jami’iyyar APC da su natsu su zabe mutumin da zai kaytatawa alumman Jihar Nasarawa, kada su zabewa alumma Jihar mutumin da zai wargaza jihar.

Advertisement
Click to comment

labarai