CMG Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Gwamnatin Birnin Shanghai Daga Duk Fannoni — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

CMG Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Gwamnatin Birnin Shanghai Daga Duk Fannoni

Published

on


Yau Litinin 8 ga wata babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin wato China Media Group (CMG) da gwamnatin birnin Shanghai sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a birnin na Shanghai, lamarin da ya alamanta cewa, CMG ya kara samun ci gaban aikinsa inda ya kara yin tasiri ga kafofin watsa labarai a duk fadin duniya.

A halin yanzu CMG ita ce kafar watsa labarai mafi girma a duk duniya, haka kuma yana taka muhimmiyar rawa a aikin rediyo da telibijin na kasar Sin, birnin Shanghai ya kasance babban birnin wanda ke sahun gaba matuka a fannin yin gyare-gyare da bude kofa ga waje da kuma samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire. A watan Yunin bana, sassan biyu wato CMG da birnin Shanghai sun taba shirya bikin nune-nunen fina-finai na kasa da kasa karo na 21 tare cikin nasara, hakan ya aza harsashi mai inganci ga hadin gwiwarsu, bisa yarjejeniyar da suka daddale, CMG za ta bude sassansa guda biyu a birnin Shanghai, wato babban ofishinsa dake yankin mashigar teku ta kogin Yangtze, inda lardunan Zhejiang da Jiangsu da birnin Shanghai suke, da kuma babban ofishinsa a birnin Shanghai. Ko shakka babu lamarin zai yi babban tasiri ga duk fadin kasar ta Sin.

CMG za ta yi amfani da albarkatun birnin Shanghai domin gudanar da hadin gwiwa mai zurfi daga duk fannoni da gwamnatin birnin, misali shirya manyan ayyukan al’adu, da samar da hidima ga yankin mashigin teku ta kogin Yangtze wato lardunan Zhejiang da Jiangsu da birnin Shanghai, da samar da shirye-shiryen telibijin masu amfani da fasahohin zamani ta 4k, da gudanar da ayyukan dake da alaka da wasannin motsa jiki, da fassara fina-finai da wasan kwaikwayo daga Sinanci zuwa harsunan waje da sauransu, haka kuma za su kara karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin watsa labarai a gida da ketare baki daya, a karshe dai CMG za ta cimma burin samun ci gaba mai inganci. (Mai Fassarawa: Jamila Zhou, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)

Advertisement
Click to comment

labarai