Ba Ma Bukatar Ka A Jam'iyyar Mu -APC Ga Fayose — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Ba Ma Bukatar Ka A Jam’iyyar Mu -APC Ga Fayose

Published

on


Jam’iyyar APC ta jihar Ekiti ta ce ma gwamna Fayose tun wuri ya neme jam’iyyar da zai koma in ya tashi ficewa daga PDP, don kuwa ba a bukatar shi a jam’iyyar APC.

Kalaman sun fito ne daga bakin Cif Paul Omotoso shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekitin a yau Talata a garin Ado Ekiti.

‘Kada Fayose ya fara tunanin sauya sheka daga PDP zuwa APC, har sai ya gama da laifukkan da ake zargin shi da tafkawa, don mun ji ana ta rade-radin wai zai dawo APC.’ inji Omotoso.

Fayose ya yi barazanar barin jam’iyyar PDP bayan ya yi zargin an tafka magude a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar, inda tsohon mataimakin shugaban kasa ya make Aminu Waziri Tambuwal, wanda su Fayose suke goyawa baya.

Tambuwal ne yazo na biyu da kuri’u 693 a yayin da shi kuma Atiku Abubakar yazo na daya da kuri’u 1,532, ‘yan takara 12 ne suka fafata a zaben fidda gwanin.

A karshe Omotoso ya shawarci Fayose da yaje ya ji da shari’arsa da take gaban kotu, inda ake zargin sa da cin hanci da rashawa da wawushe kudin jihar Ekiti, saboda a cewarshi APC ba mafaka bace ta masu laifi, kuma lallai Fayose ya kwana da sanin bashi da wajen zama a jam’iyyar.

Advertisement
Click to comment

labarai