Cinikayya Tsakanin Nijeriya Da Tarayyar Turai Ta Kai Naira Tiriliyan 8.9 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Cinikayya Tsakanin Nijeriya Da Tarayyar Turai Ta Kai Naira Tiriliyan 8.9

Published

on


Jimlar cinikayya tsa kanin Nijeriya da kungiyar nahihar turai EU ta kai  biliyan  25.3 na kudin Euros kimanin  naira tiriliyan  8.9 a shekarar 2017. Bayanin ha kan ya fito ne dzga bakin Mataimakin tawagar EU da kuma kungiyar ECOWAS Mista Richard Young,

Richard Young ya sanar da ha kan ne a taron manema labarai a kan harkar cinikayya tsa kanin Nijeriya da EU a jihar Legas/inda ya ce anyi ha kan ne domin kara kulla zumunci tsa kanin kamfanonin dake Nijeriya da EU. Tawagar ta EU, kasashen dake cikin EU da kuma kamfanonin na EU, tuni sun kafa kungiyar kasuwanci mai suna EBO wadda kuma take wakiltar kamfanonin nahiyar ta turai a fanninoni tattalin arzikin Nijeriya da ban-da-ban dake Nijeriya.

Kungiyar ta EBO a Najriya, zata tabbatar da samar da tsari na tattaunawa da hukumon dake Nijeriya da kamfanoni masu zaman kansu da nufin ciyar da kasuwanci a gaba, zuba jari da kuma kara kulla dangantaka tsa kanin Nijeriya da EU.

Young yaci gaba da cewa, EU ta kuma kaddamar da zuba jari na waje mai suna EIP don bayar da kwarin gwarin gwaiwa wajen zuba jari a kasashen data yi hadaka dasu harda Nijeriya, inda ya ce, ta hanyar EIP din za kuma a kara karfafa dangantaka yadda za:a samar da ci gaba da kuma samar da ayyukan yi don a rage yadda ake yawan fitar bakin haure kwarara  zuwa nahiyar ta turai.

Acewar sa, EIP din sabon shiri ne yadda za’a taimaka wajen samar da ci gaba ta hanyar zuba jari haka zata kuma kara samar da hanyar zuba kudi a bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen zuba jari.

A karshe ya ce, sai dai sabon EIP din zai kara samar da zuba jari da kuma jurewa ko wanne irin yanayi har ila yau, taron na EU karo na bakwai zai samar da kyakawan yanayi da kuma a kan tsrin da gwamnatin ta samar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai