Dan-Iya Ne Dan Takarar PDP A Sokoto Ba Tambuwal Ba -Ibrahim Milgoma — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Dan-Iya Ne Dan Takarar PDP A Sokoto Ba Tambuwal Ba -Ibrahim Milgoma

Published

on


Ciyaman din Jam’iyyar PDP na jihar Sokoto ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa, cewar ba Alhaji Mannir Dan-iya bane dan takarar mukamin gwamna na jam’iyyar a jihar Sokoto, wai an canja shi da gwamna mai ci, wato Tambuwal.

Milgoma ya kara da cewa lallai jam’iyyar PDP ba ta sauya dan takarar ta ba, duk da akwai sauran lokaci da doka ta tanada don sauya dan takarar, amma dai zuwa yanzu jam’iyyar bata canja ba.

Jam’iyyar zata bayyana a hukumance inda wani sauya da tayi ko take shirin yi, kuma jam’iyyar zata tabbatar ta bi dukkan ka’idojin da suka dace kafin ta dau wani mataki anan gaba.

Taron da aka yi a babbar sakatariyar jam’iyyar ta jiha, taro ne da aka shirya don yabawa wakilin jam’iyyar game da yadda suka goya ma gwamna Tambuwal a zaben fidda gwani na takarar shugabancin kasa da aka gudanar a garin Fatakwal.

Advertisement
Click to comment

labarai