Dalilin Mu Na Kin Sake Zaben Buhari Karo Na Biyu - Dokta Shamusddeen — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Dalilin Mu Na Kin Sake Zaben Buhari Karo Na Biyu – Dokta Shamusddeen

Published

on


Garkuwan Makarantan Zazzau, kuma Shugaban Kungiyar National Youth Empowerment Initiative Organization of Nigeria, matashin dan siyasa ne dan gwagwarmayar kwato wa matasa ‘yanci, a tattaunawarsa da Leadership A Yau ya bayyana yadda ake yin amfani da matasa wajen darewa madafun iko, sannan daga bisani a yi watsi da su:

Me za ka ce game da mulkin Jam’iyyar APC? Mun gode wa Allah da Ya sa muka kusa zuwa karshen mulkin lafiya, kuma Allah Ya canja mana shi da mafi alheri. Amma gaskiya matasa ba za mu sake zaban APC ba.

Kuma idan za a yi zaben Shugaban Kasa yau, sai APC ta riga rana faduwa insha Allah. Domin duk alkawuran da ta dauka wa matasa ba ta cika ba. Da yawa daga cikin matasa akwai wadanda dako suke yi, don dai mu zama ’yan kasa na gari. Kuma duk da muna samun kudi da wahala, haka matasa suka rika tura wa Buhari kati domin ya samu kudin kamfe. Shugaban Kasa ya yi mana alkawarin da mu za a yi mulki saboda muke da kashi 68 cikin 100 na jama’ar Najeriya, Wadanda kuma ba su da aikin yi za a rika ba su Naira dubu 5 duk wata, amma abin sai ya zama ko Ministan Matasa da Wasanni tsoho aka ba. Sai ana amfani da wadansu matasa a matsayin sojojin baka, idan dattawan kasa ko iyayen kasa sun ja hankalin gwamnati sai su je kafafen labarai suna zaginsu.

Ba ka ganin gwamnatin ta cika alkawari a fannin zaman lafiya? Bari in fada maka bambancin mulkin Buhari da na Jonathan a kan tsaro; lokacin Jonathan ’yan jarida na fadin kowane labarai da ya faru a kasa, amma yanzu kun daina. Shi ya sa wanda abin bai kai kansa ba sai ya yi zaton an samu tsaro ko kuma ida an fada masa sai ya yarda. Sannan Jonathan ya fi Buhari girmama doka, domin akwai shari’a da yawa tsakanin gwamnati da mutane dake gaban kotu, kuma kotun ta bukaci a saki wadansu ko a bayar da belinsu amma gwamnati ta ki, don kawai wata manufa.

A yankin Arewa maso Gabas an samu zaman lafiya? Ka je Arewa maso Gabas din ka gane wa idonka, ka daina aiki da maganganun sojojin baka wadanda ke zuwa kafafen watsa labarai su yi karyar an samun tsaro domin kawai a ba su kudi. Na fada maka labari aka daina kawowa na ainihin abin da ke faruwa. A bangaren ilimi a matsayinka na Garkuwan Makaranta, me za ka ce? Ilimin ma da yana da baki da sai ya yi karar wannan gwamnati. Malamai fa ake Kora ana cewa sun kasa cin jarrabawa. Su kuma dalibai ana mayar da su almajirai karfi da yaji, domin yaro zai je makaranta ba a inganta masa ilimi ba, ba a ba shi kayan karatu ba, ba a ma biya malamin albashi ba, amma an zo ana sam masa alale da biskit a lokacin karatu. Shi ya sa wani yaron da ya karba sai ya koma gida a guje. Ka ga bai ma zauna a cikin aji ba balle a koya masa karatun balle kuma ya yi karatun ya fahimta ballantana nan gaba ya zama shugaba. Kuma ina kira ga wadanda nake jagora da sauran matasan kasar nan duk wanda ya ba ku kudi don ku zabe shi, to, ku karba amma kada ku zabe shi, ku dubi cancanta. Amma Buhari bai ma cancanta ba, don haka kada mu sake zabarsa.

Me za ka ce game da batun canja sheka da ’yan siyasa ke yi? A fahimtata, karairayi ne suka yi musu yawa suke ganin canja sheka zai fiye musu sauki, ko ba komai idan matasan Najeriya suka gane sanatoci da ’yan majalisa ba sa tare da Shugaban Kasa suna iya kara zabarsu.

Ba ka ganin yawancinsu ba don mutane suke canjawar ba? Akwai wadanda don talaka suke yi tunda sunyi kokarin a taimaki talaka musamman matasa an ki, shi ya sa suke canja sheka domin matasa ba sa tare da APC, kuma matasan, mu ne muka fi yawa. Duk mazaba muna da mabiya da jagora kuma akwai shugaban karamar hukuma sannan muna daja gora na jiha, akwai kuma shugabannin yanki, sannan kuma ni ne jagora na kasa baki daya. Ba mu yanke wace jam’iyya za mu yi ba, amma tabbas duk jam’iyyar da za mu bi, za mu hada kuri’un matasa wuri daya domin mu ci gajiyara bin. Ko ba komai a yi mulki da matasa.

Advertisement
Click to comment

labarai