Mako Guda Da Zaben Fidda Gwani: APC Ta Fitar Da Sunan Sanatocin Da Ta Tsayar A Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Mako Guda Da Zaben Fidda Gwani: APC Ta Fitar Da Sunan Sanatocin Da Ta Tsayar A Bauchi

Published

on


Bayan mako guda da yin zaben fidda gwani na Sanatoci a jam’iyyar APC a jihar Bauchi, kwamitin da ya jagoranci gudanar da zaben ya fitar da wadanda APC ta tsayar don neman kujerun daban-daban.

LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar an gudanar da zaben Sanatoci a ranar Laraba 3/10/2018, inda aka gudanar da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Alhamsi 4/10/2918 da kuma gudanar da zaben ‘yan majalisun dokokin jihar ta Bauchi a ranar Juma’a 5/10/2018.

A wata sautin murya da ya aike wa al’umman jihar Bauchi ta kafar sadarwar zamani, shugaban kwamitin gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Bauchi na APC; Farfesa Bakori Muhammad ya shaida cewar jerin ‘yan takarar da suka fitar din sun kunshi ‘yan takaran kujerar Sanatoci uku da suke Bauchi, ‘yan majalisun wakilai ta tarayya 12; da ‘yan majalisun dokokin jihar Bauchi su 21.

Duk da yake a sautin muryar na shugaban zaben bai ayyana adadin kuri’un da wadanda suka fitar din suka ci a lokacin zaben ba, illa dai ya jero sunayen wadanda suka tsayar da za su wakilci jam’iyyar a zaben da tafe na 2019 a jihar ta Bauchi.

Wakilinmu ya shaida mana cewar gaza fitar da sakamakon zaben a jihar ta Bauchi tun bayan da aka yi ya haifar da zafafan muhawara da yaduwar jita-jita a tsakanin jama’an jihar ta Bauchi, inda bangarori daban-daban suka yi ta ikirarin sune suka ci, hakan kuma ya jefa wasu ‘yan takara a cikin shakko da fargaba.

Duk da yake Bakori bai kuma bayyana adadin kuri’un da aka kada da wadanda aka kayar ba, balle ya jero sunayen wadanda aka kayar a lokacin zaben, a cikin sautin muryarsa ya yi bayanin cewar wadannan jerin da suka fitar su ne APC ta sahalesu da za su wakilceta.

Ya kara da cewa; “Ni Farfesa Ahmed Bakori Muhammad; shugaban kwamitin zabuka da aka yi na jam’iyyar APC na jihar Bauchi; kama daga majalisar dattajai, majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar ta Bauchi.

Ya shaida cewar sunayen wadanda za su yi wa jam’iyyar APC takara da cewar su ne kamar haka, Sanatan Bauchi ta Kudu sun tsaida Hon. Lawan Yahaya Gumau; Sanatan Bauchi ta tsakiya, Hon. Halliru Dauda Jika sai kuma mazabar Bauchi ta Arewa APC din ta tsayar da Adamu Muhammad Bulkaciwa a matsayin dan takararta da tsaya domin ya nema mata sa’a a babban zaben 2019.

Ahmed Bakori ya kuma jero wadanda za su tsaya wa APC a kujerar majalisar wakilai ta tarayya a dukkanin fadin jihar ta Bauchi da suka hada da; Bauchi ta tsakiya Kwamared Sabo Muhammad; mazabar Alkaleri/Kirfi, Musa Muhammad Pali;Dass/Tafawa/Bogoro, Dalhatu Abubakar Abdullahi; mazabar Toro, Umar Muda Lawal; Ganjuwa/Darazo kuma APC ta tsaida Mansur Manu Soro ne; Ningi/Warji, Abdullahi sa’ad Abdulkadir; Jama’are/Itas, Bashir Uba.

Shugaban kwamitin zaben ya ci gaba da bayyana jerin wadanda suka samu nasarar da cewar a mazabar Katagum, sun amincewa Ibrahim Baba; Zaki, Tata Umar; Gamawa, Muhammad Garba Gololo; Misau/Dambam, Hon. Ibrahim Makama;Shira/Giade, Kani Abubakar Faggo, inda ya shaida cewar wadannan sune za su shiga a dama da su wajen neman kujerun ‘yan majalisun tarayya a karkashin APC.

Farfesa Bakori Muhammad ya kuma shaida cewar a majalisar dokoki na jihar Bauchi, ita jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta tsayar da ‘yan takararta kamar haka; inda ya fara da karamar hukumar Alkaleri, da cewar a mazabar Duguri/Gwana, Hassan A. Abdullahi; 3 Alkaleri/Pali, Yusuf Muhammad Bello.

Bakori ya shaida cewar a cikin karamar hukumar Bauchi kuwa, APC ta tsayar da Kwamared Aliyu Abdullahi Ilelah a mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dokokin jihar Bauchi; Zungur/Galambi da Miri, Abdulhamid Rufa’i.

Cikin karamar hukumar Bogoro kuwa, Arkila Semon Taimako; Dambam/dambam, Baballe Abubakar B; Darazo ta tsakiya Honorabul Kawuwa Shehu Damina; Darazo/Sade, Bello Haruna; Dass/Dass Najumuddin Garba; Gamawa ta tsakiya; Bello Sarkin Jadori; Gamawa/Udubo, Umar Yakubu; Ganjuwa ta Yamma, Yusuf I. Dadiye; Ganjuwa ta Gabas, Garzali Abubakar; Giade/Giade, Gani Umma Bello; Itas/Dadau, Honorabul  Rabi’u Bala Cash; Jama’are/Jama’are, Sale Muhammad; Katagum/Azare/Madangala, Hon.Tijjani M. Aliyu; Chinade/Madara, Ibrahim Jibo; Kirfi/Kirfi, Ibrahim Galadiman Badara.

Sauran sune; Misau/Chiroma, Sadik Ahmed Iliyasu; Misau/Hardawa, Adamu Ahmed Hardawa; Ningi/Ningi ta tsakiya, Abubakar Y. Sulaiman; Ningi/Burra, Ado Wakili; Shira/Shira, Bello Mu’azu; Shira/Disina, Yakubu Ali; Tafabalewa/Lere/Bula, Muhammad Dauda; Toro/Jama’a, Tukur Ibrahim; Toro/Lame, Bala Abdulllahi Rishi; Warji/Warji, Yunusa Ahmed; Zaki/Zaki, Muktar A. Suleiman; Zaki/Sakuwa, Abdullahi Bello.

Bakori ya kara da cewa, “Wadannan sune za su yi takara a jam’iyyar APC a zabe mai zuwa a shekara mai zuwa,” Inji Bakori Muhammad Kawo zuwa yanzu dai bamu samu labarin cewar ‘yan takarar da suka shiga cikin neman sa’arsu APC din ta sanar da su sakamakon zaben ta hanyar da kai tsaye daga jam’iyyar ba, inda kowa ya wayi gari da ganin sakamako walau wadanda suka ci ko akasin haka.

Tun dai bayan gudanar da zaben da rashin bayyana sakamakon zaben wanda babu wanda ya san dalilin kwamitin zaben na kin bayyana sakamakon zabukan a lokacin da ya dace, ‘yan takara sun yi ta zaman jiran tsammani daga karshe dai sun riski wannan sakamakon a kafar sadarwar zamani.

 

Advertisement
Click to comment

labarai