Manomi Ya Yi Wa Tsohuwa ’Yar Shekara 78 Fyade A Neja — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

NOMA

Manomi Ya Yi Wa Tsohuwa ’Yar Shekara 78 Fyade A Neja

Published

on


Wata kotun majastare a garin Munna ta bayar da umurnin a garkame wani manomi dan shekara 32 mai suna Rilwanu Salisu, bayan da ya amsa cewa, ya yi wa wata tsohuwa ‘yar shekara 78 fyade. An gurfanar da Salisu ne a karkashin dokar fanal kot mai lamba 282. Mai gabatar da kara daga rundunar ‘yan sanda mai suna, Mista Daniel Ikwoche, ya ce,  dan tsohuwar da aka yi wa fyaden mai suna, Mukhtar Garba, ya kai kara ne ofishin ‘yan sanda dake unguwar Nasko a ranar 14 ga watan Satumba.

Ikwoche ya bayyana cewa, mai karar ya yi wa ‘yan sanda bayanin cewa, wanda ake zargin mazaunin kauyen Kwada dake a karamar hukumar Magama ya shigo gidansu ne inda ya same ta tana barci ya kuma danneta inda ya lalata da ita da karfi da yaji.

Ya kuma kara da cewa, mai karar ya ce, a kokarin yin lalatar da ita sai da ta ji ciwo a al’aurarta har yana zubar da jini.

Da aka tuhume shi a kan laifin, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ya kuma nemi kotu ta yi masa ahuwa.

Amma mai shari’a, Nasiru Muazu, ya ki sauraron bukatar wanda ake zargin saboda kotunsa bata da hurumin sauraron kara gaba daya saboda ta shafi fyade, fyade kuma babban kaifi ne a dokar kasa.

Daga nan Muazu ya bukaci dan sanda mai gabatar da kara ya mika takardar kara zuwa ofishin mai gabatar da kara na jiha don a bayar da shawar yadda za a fuskanci sharia’a.

Daga nan ne ya umurci a wuce da wanda ake zargin zuwa gidan yari kafin a ji sakamakon shawarar, ya kuma daga karar zuwa ranar 25 ga watan Oktoba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai