Rashin Nagartar Shugabanci Na Iya Zamar Wa APC Tarnaki -Wanna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Rashin Nagartar Shugabanci Na Iya Zamar Wa APC Tarnaki -Wanna

Published

on


An bayyana cewar rudu da rashin shugabancin jam’iyya na hakika na shirin mayar da hannu agogo baya ga jam’iyyar duba da irin yadda aka gudanar da zabukan cikin gida da matsayin da jam’iyyar ke ciki a halin yanzu. Shugaban tallata muradun gwamna Abu Lolo da shugabanci na gari, Alhaji Awaisu Muhammadu Giwa ne ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a minna.

Awaisu Giwa ya ce idan APC na bukatar samun saukin fuskantar babban zabe mai zuwa ya zama tilas tayi adalci ga wadanda sukai takarar na bai wa wadanda suka samu galaba takarar su tare da adalci ga wadanda suka fadi zabe ta hanyar mayar masu da kudaden su na fom domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Idan rahotanni da ke yawo ya tabbata na bai wa wasu ‘yan majalisun tarayya takarar kai tsaye alhalin ba su ne jama’a suka zaba ba to lallai za a yi kitso da kwarkwata wanda ba zai haifar da da mai ido ba, domin jama’a sun kada wadannan mutanen ne saboda rashin katabus din su a lokacin suna majalisa, ya sa ganin an

bai wa jama’a damar zabin abin da suke so suka wancakalar da su tare da zabo wadanda suke kyautata zasu yi masu aiki, amma matsayin da uwar jam’iyya ke shirin dauka lallai an bar tsarin Dimokradiyya.

Da farko ita kanta kundin tsarin APC ta shigo da danbarwa na cewar an amince da zaben kato bayan kato ko in ce ‘yar tike, ko kuma anfani da dalaget ko kuma sulhu tsakanin ‘yan takara kuma aka ce an bai wa jahohi bin zabin da suke so. Hakan sai ya bai wa wasu damar yin kadan tsaye wa shugabancin jam’iyya, domin abin da muka sani a tsarin shugaban siyasa na gaskiya ko shugaban kasa bai isa ya yiwa shugabancin jam’iyya shishshigi balle wani dan jam’iyya can a gefe ya rika daukar matsayi na yi wa dokokin jam’iyya karan tsaye ba.

Domin in ka duba halin da jam’iyyar ke ciki yau abin tausayi ne, shugaban jam’iyya Adams Oshiomhole yana da matsayar da ya dauka, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da matsayin da ya dauka, tsohon gwamna Bola Ahmed Tinubu yana da matsayin da ya dauka shin ina shugabancin yake, ya zama wajibi abin da ya shafi jam’iyya a bar shi ga shugabannin jam’iyya, abin da ya shafi gwamnati a bar gwamnati ta yi aikinta, amma idan abin da su Tinubu ke shirin aikatawa ya tabbatar to lallai shugabanci APC ya koma baya.

Idan an san abin da ake shirin aikatawa yau ya tabbatar to lallai an yi wa APC rashin adalci kuma lallai akwai lauje cikin nadi domin za a mayar da siyasar baya, mai makon tafiyar ta wuce inda take yau sai ya zama na tsarin siyasar baya har yana son fin na yanzu tsari da kwarjini, ya zama dole in har ana son kawo sauki ga halin da ake ciki yanzu a tabbatar wadanda aka sayarwa fom kuma suka fadi zabe a mayar masu da kudaden su na fom, domin duk yadda ka ke ganin rashin tasirin mutum a siyasa yana da hanyar da zai iya yi maka illa ganin yana da magoya baya.

Amma ban gamsu da rahotannin da ke yawo ba, wai ana  son bai wa ‘yan majalisun tarayya da suka fadi zabe tikitin kai tsaye na takara ba ke nan har yanzu ba mu kama turbar siyasar ba da gaskiya ba. Ya zama wajibi shugabancin APC ta yiwa kanta kiyamullaili ta dawo cikin hayacinta da kanta kafin yankin hula ya kai ta dare, domin wannan hanyar ba mai dorewa ba ne da ta ke shirin fadawa, talaka ya zabi abin da yake so ya zama wajibi a ba shi damar jarabawa domin suna ganin wadanda suka kawar sun kasa.

Giwa ya ce ko lokacin mulkin Alhaji Shehu Shagari ba a yiwa jam’iyya karan tsaye kamar yau yadda muke gani a APC ba, lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu da su kawo karshen irin abubuwan da suke yi, ya kamata ne su karfafawa jam’iyya ba wai su rika yi mata kutse ba, domin maganar gaskiya idan aka tafi a hakan ya nuna cewar babu shugabancin a jam’iyyar APC domin kowa ma na iya takara yadda yake so dan mulki na hannu shi, ya zama wajibi APC tayi gyare gyare a cikin dokokin ta duk abin da zai iya janyo ma ta rashin kima a idon jama’a ta kauce ma shi tun da sauran lokaci, amma akan matsala daya a ce akwai matakai har uku kuma an bai wa jahohi damar daukar duk wanda su ke so wannan ba daidai ba ne, idan maganar dalaget ko sulhu tsakanin ‘yan takara ne wannan abu ne mai kyau, amma an ce an bai wa jiha yin ‘yar tike ko dalaget ko sulhu kuma bayan sun kammala uwar jam’iyya tada kafa tayi fatali da hakan wannan kuskure ne babba.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai