Tsofaffin ’Yan Majalisa 10 Ne Suka Koma Kujerunsu A Katsina — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Tsofaffin ’Yan Majalisa 10 Ne Suka Koma Kujerunsu A Katsina

Published

on


Tafoki shi da wasu tsofaffin ‘yan majalisar jihar Katsina tara daga cikin 34, zuwa yanzu sune suka samu nasara a zaben fidda gwani, na jam’iyyar APC, anda kuma hakan ne ya basu dama ta sake tsayawa a zabe su a wa’adi na biyu a shekarar 2019.

Jaridar LEADERSHIP A Yau ta samo labarin cewa takwas daga cikin ‘yan majalisun ba su sayi fom na nuna bukatar tsayawa takara ba, na jam’iyyar, yayin da kuma wasu hudu, basu samu nasara ba lkacin da aka yi zaben fidda gwani makon daya wuce.

Majiyarmu ta labarta mana cewar an daina yin zabe a mazabu biyu ranar Lahadi, har sai shekaran jiya, saboda matsalar da aka samu a karamar hukumar Batsari, daga nan kuma kayayyakin zabe ba a kawo su da wuri ba a karamar hukumar Bakori, amma kuma daga baya al’amarin ya tafi ba wata matsala.

Sakamakon da aka bada sanarwa lokacin da aka kammala jefa ita kuri’ar,a kananan hukumomi daban daban, an bayyana cewar Ahmed Abubakar Adidas shi ya samu nasara a (Mai’adua) Nasir Yahaya b(Daura) Abubakar Mohammed (Funtua) Haruna Aliyu Yamel (Dutsi) Lawal Isa (Charanchi) Garba Ya’u (Kankara)da kuma Salisu Hamza Rimaye (Kankia) da dai sauran wadanda basu samu nasara a mazabunsu ba.

Hakanan shi ma kakakin majalisar jihar Katsina Abubakar Yahaya Kusada wanda ya tsaya a mazabar dan majalisar akilai ta tarayya ta Kusada /Ingawa / Kankia maimakon mazabar Kusada, a majalisar jihar Katsina, shi ma ya samu nasara.

Amma kuma su abokan nashi Salisu Haruna (Mashi) Kabir Lawai (Kurfi) Yunusa Idris (Musawa) su da wasu su, basu samu nasara ba, yayin da shi kuma mai wakiltar Batsari shi ya janye, daga ita takarar bayan da aka samu wata matsala dangane da zaben ranar Asabar.

Leadership Ayau ta bayyana cewar sakamakon Bakori da Batsari a lokacin ba a kammala shi ba, sabodac akwai wasu al’amuran da ba a gama su ba.

Da aka tuntubi shugaban zabubbukan fidda gwani a jihar Dakta Isa Adamu wanda ya bada bayanin cewar ana bayar da sakamakon zabubbukan a mazabun da aka yi, duk da yake dai a alokacin ana gudanar da zaben a Batsari da kuma Bakori, amma kuma ba a, bada bayani ba akan cikakken bayanin akan shi zaben.

 

Advertisement
Click to comment

labarai