2019 : Dantakarar Gwamnan Jigawa A PDM Ya Sha Alwashin Kayarda Gwamna Badaru — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019 : Dantakarar Gwamnan Jigawa A PDM Ya Sha Alwashin Kayarda Gwamna Badaru

Published

on


Dantakarar neman gwamnan jihar Jigawa a jam’iyyar PDM  Alhaji Sanusi Muhammed Gumel ya sha alwashin kwace mulkin jihar Jigawa daga hannun gwamna mai ci Alhaji Badaru Abubakar a kakar zabe mai zuwa ta 2019.

Gumel ya yi wannan furuci ne jim-kadan bayan lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudunar a babban birnin jihar dake Dutse.

Haka kuma dan takarar gwamnan ya soki shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan jihar ta Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru bisa gazawa wajen tabuka kamai duk da kwashe ysawon shekaru hudu da suka yi suna mulkin al’ummar wannan kasa.

”Ko tantama babu shugaba Buhari da gwamna Badaru sun gaza sauke nauyin da al’umma suka dora musu, musamman duba da yadda rashin aikin yi ga matasa ke karuwa, tabarbarewar ilmi, rashin baiwa manoma da masu kananan sana’o’i tallafi na hakika‎ gamida tabarbarewar fannin lafiya musamman ga talakawan wannan kasa” inji Gumel.

‎annan ya sha al’washin cewa, matukar al’ummar wannan kasa suka basu dama ta hanyar jefa musu kuru’u a zabe mai zuwa to babu ko shakka jam’iyyarsu ta PDM zata kai wannan kasa da al’ummar ga gaci.

Shi kuwa da yake nasa jawabin, mukaddashin shugaban jam’iyyar ta PDM a jihar ta Jigawa, ‎Alhaji Sule Idris Hadejia ya bayyana sunayen wadanda suka yi nasarar lashe zaben fidda gwani a jam’iyyar wadanda suka hadarda,Alhaji Sanusi Muhammed Gumel a matsayin dan takarar gwamnan jihar,Alhaji Auwalu Abdullahi Bayero dan takarar Sanata a yankin Arewa maso yamma na jihar, Sule Idris Hadejia a mazabar Jigawa ta Arewa maso gabas da kuma Alhaji Jamilu Ubale a Jigawa ta tsakiya.

 

Advertisement
Click to comment

labarai