A Yau Mourinho Zai San Makomarsa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

A Yau Mourinho Zai San Makomarsa

Published

on


Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa a yau Alhamis kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zai zauna da shugaban gudanarwar kungiyar, Ed Woodward domin sanin makomarsa Mutanen biyu dai babu wata alaka mai karfi a tsakaninsu tun bayan da kungiyar ta kasa siyowa Mourinho ‘yan wasan dayace yana bukata a kawo masa wanda sakamakon hakan Mourinho ya dinga sukar shugaban gudanarwar. Rashin kokarin kungiyar ta Manchester United yasa aka fara rade radin cewa kungiyar za ta koreshi idan bai samu nasara ba a wasan da kungiyar ta buga da Newcastle a ranar Asabar din data gabata. Sai dai duk da nasarar da United din tayi a wasan na ranar Asabar babu tabbas din ci gaba da zaman Mourinho idan kungiyar bata ci gaba da samun nasara ba a ragowar wasanni kamar yadda rahotanni suka bayyana. Tattaunawar dai itace za ta bayyanawa Mourinho makomarsa kuma zai san matsayin kungiyar na neman wanda zai maye gurbinsa idan har kungiyar da gaske tana da niyyar sallamarsa daga aiki. Manchester United dai za ta buga wasan firimiya na gaba da kungiyar Chelsea daga nan kuma za ta fafata da kungiyar Jubentus a gasar zakarun turai gida da waje kafin kuma wasan hamayya da Manchester City.

Advertisement
Click to comment

labarai