Abu Ne Mai Wahala A Samu Wanda Zai Maye Gurbin Ronaldo A Duniya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Abu Ne Mai Wahala A Samu Wanda Zai Maye Gurbin Ronaldo A Duniya

Published

on


Darakatan wasanni a kungiyar kwallon kafa ta Juventus Fabio Paratici, yace zai yi wahala a iya samun wanda zai iya maye gurbin zakakurin dan wasa kamar Cristiano Ronaldo a duniya nan gaba.

Paratici ya bayyana haka ne jim kadan bayan karbar kyautar girmamawa ta mafi kwazon daraktan wasanni a tsakanin takwarorinsa da ke kungiyoyon gasar Seria A, a kasar Italiya.

Yayin da yake zantawa da manema labarai dangane tasirin sauyin shekar Ronaldo zuwa Juventus daga Real Madrid, Paratici, yace kungiyar za ta ci gaba da marawa Ronaldo baya domin kare mutuncinsa, dangane da zargin aikata fyade da wata mata ke yi masa.

Darakatan wasannin na Juventus, ya kuma musanta rahotannin dake cewa, kungiyar na shirin maido da tsohon dan wasanta Paul Pogba, wanda a yanzu yake bugawa Manchester United wasa, bayan sauyin sheka zuwa kungiyar daga Juventus a shekarar 2016, kan kudi fam miliyan 89.

Sai dai yace basu taba tunani akan dawo da Pogba ba amma kuma a kwallon kafa komai yana iya kasancewa idan har mutum yana raye kuma har yanzu akwai alaka mai kyau tsakaninsu da Pogba.

Sannan yace kungiyar ta Juventus za ta ci gaba da siyo manyan ‘yan wasa a duk inda suke a duniya domin ganin kungiyar ta mamaye kwallon kafar duniya.

Advertisement
Click to comment

labarai