An Cafke Wani Magianci Da Damfarar Naira Miliyan 1.4 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Cafke Wani Magianci Da Damfarar Naira Miliyan 1.4

Published

on


A ranar Laraba ne aka gurfanar da wani mutum a gaban wata kotu a Tinubu dake jihar Legas, mai suna Ibrahim Osuolale dan shekara 37, wanda yake sama wa mutane takardar tafiye-tafiye, bisa zargin damfarar naira miliyan 1.4. Osuolale wanda yake zaune a titin Olatunji cikin yankin Medina a unguwar Igando Egan dake jihar Legas, ya bayyana a gaban alkali A. M. Olumide-Fusika inda ake tuhumar sa da laifuffuka guda biyu, laifin danfar da kuma laifin sata, inda duk ya musantan. Alkali mai shari’a ya bayar da belin wanda ake zargi a kan kudi naira 500,000 tare da masu tsaya mashi mutum biyu. Tun da farko dai, lauya mai kara sufeto Ben Ekundayo ya fadawa kotu cewa, wanda ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Yuli da misalin karfe 8 na safe a cikin rukunin gidaje wanda ake kira da suna ‘Good Homes Estate’, dake layin Angelia Lane dake Addo na jihar Legas. Ana dai zargin sa da danfarar Miss Chinenye Ibekwe naira miliyan 1.4, domin ya taimake ta a kan ya sama mata takarda izinin shiga kasar Kuwait, Austalia da kuma kasar Singapore. Ya kara da cewa, Ibekwe ta hadu da wanda ake zargi ne a kafan sada zumunta na ‘WhatsAPP,’ inda ya bayyana kansa a matsayin jami’i mai samar wa mutane takardar tafiye-tafiye.

“Da Osuolale ya amsa kudin, sai ya tsere daga mazauninsa sannan kuma ya daina daga wayarta.

“Ibekwe ta tafi ofishin jakadanci na kasar Kuwait da kuma na kasar Australia domin ta bincika, sai aka tabbatar mata da cewa ba a nemi takardar izinin shiga kasar da sunan da ta ba da ba.

“Wanda ake zargi dai ya ijeye fasfo din da Ibekwe ta bashi a wata mashaya dake kusa da gidanta, inda a nan ne aka ganshi sannan aka damke shi,” inji Ekundayo.

Laifin dai ya saba wa sashe na 287 da na 314 na tsarin mulkin jahar Legas ta shekarar 2015, kowani sashi yana dauke da hukuncin daurin shekara 15 a gidan kaso. Alkali mai shari’a ya dage zaman shari’ar har sai ranar 23 ga watan Oktoba. An Dakile Kokarin Safarar ‘Yan Mata 8 Daga Ghana A Filin Jirgin Sama Na Legas

Jami’an shige da fice ta Nijeriya sun dakile kokarin safarar ‘yan mata guda 8, a filin jirgin Murtala Muhammed dake jihar Legas. An dai cafke wadanda ake zargi ne ranar Litinin a filin jirgin na jihar Legas, lokacin da suke kokarin zuwa kasar Kuwait inda daga nan sai su shiga kasar Libya sannan kuma sai su yi kasar Turai da su. Jami’an shige da ficen sun dai samu nasarar cafke wadanda ake zargi ne lokacin da suka binciki wata yarinya, sannan suka same ta da fasfo din kasar Ghana kuma ita ‘yar Nijeriya ce. An dai bayyana wa jami’an cewa ‘yan matan masu shekaru 20 zuwa 25 suna so daga Nijeriya sai su shiga kasar Turai. Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan matan sun fito ne daga kasar Togo da kuma kasar jamhuriyar Benin bisa tallafawar wadanda suka taimaka masu. A cewar majiyarmu,‘yan matan ba su da wata dalilin yin amfani da kasar Nijeriya zuwa kasar Turai. Majiyar ta kara da cewa,“lamarin ya janyo hayaniya da jami’an. Lokacin da aka tambaye su, sai suka yi ikirarin cewa su masu gaskiya ne kuma za su je kasar Turai ne, amma za su fara sauka a kasar Kuwait. Lokacin da aka bincika sai aka samu cewa, ‘yan matan sun shigo Nijeriya ne ta hanyar mota daga kasar Ghana, inda suka shiga kasar Togo sannan suka zarce zuwa kasar jamhuriyar Benin.

“Wannan ba shi ne karo na farko wanda muka dakele safarar mutane a filin jirgi ba, sannan kuma rundunarmu za ta ci gaba da kula wa domin mu tabbatar da cewa mun dakele wannan mummunar lamarin.”

Jami’in hudda da jama’a na hukumar shige da fice Sunday James ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Rundunar tamu samu nasarar cafke mata guda 8 ‘yan asalin kasar Ghana, za mu mika su ga hukumar dake yaki da safarar mutane ta kasa domin gudanar da cikikkyan bincike,” inji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai