An Karfafi Gwiwar Mata Kan Zaben 2019 A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

An Karfafi Gwiwar Mata Kan Zaben 2019 A Nijeriya

Published

on


Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da na Tarayyar Turai sun karfafi natan Nijeriya akan zaben 2019.

Sun dai karfafi matan ne a lokacin taron cin abincin Safe da wakilan suka shirya ma mata ‘yan siyasa wanda suka fito daga jam’iya daban-daban a Babban Birnin tarayya Abuja.

Sun ba mata shawara akan cewa, ya kamata su dage wajen yin gogayya da takwarorinsu maza, wajen amsan mukamai a wannan siyasar da ake fuskanta.

Wakilin tarayyan turai, Mista Richard Young, Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, ya nuna takaicinsa da cewa kwata-kwata mata masu rike da mukamai kashi Shida ne kawai cikin Dari a Nijeriya.

Ya ce; “don haka gaskiya akwai babban aiki a gaban Matan wajen kara jajircewa don yin kafada da kafada da Maza a Nijeriya. domin wannan hakkin ku ne amma kuma kuna wasa da wannan hakin naku, ga shi nan kuma kullun Mazan kara danne ku suke yi.”

Ya kara da cewa”in dai aka ba mata dama to, za su ba da gudummmawa wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya, su kuma kawar da fatara a cikin al’umma.

Mai wakiltar Mata a Majalisar Dinkin Duniya, Misis Comfort Lamptey a nata jawabin a wurin taron, ta bayyana fatan cewa; “muna sa ran mu ga kyakkyawar canji a wurin mata a wannan Siyasar na 2019, don gaskiya in dai ana so aga canji to, dole ne a tafi da matasan mata a cikin Siyasa, ya kamata tun yanzu a fara koyar da matasan Mata harkar Siyasa, saboda su sami kwarewa ta musamman, dan idan tsofaffin hannu sun wuce sai su maye gurbin su.

Dan haka za mu ba mata goyon baya dari bisa dari a harkar Siyasa a Najeriya”.

Ambasadan Denmark a Nijeriya, kuma mai fada da nuna babbancin jinsi a Majalisar Dinkin Duniya, Mr.Torben Getterman, a sakon shi a wurin taron, ya ce idan aka yi la’akari da yawan jama’ar da suke Nijeriya to, za’a fahimci cewa lallai an tserema mata a wurin Siyasa. Dan haka da gaski muna shawartar Mata akan cewa su shiga harkokin siyasa a Nijeriya a dama da su.

Ya kara da cewa”Mata a Nijeriya suna da matukar yawa, amma sai dai su buge da jafama Maza kuri’a su ba za a jefa musu ba, gaskiya yana da matukar mahimmanci su gane wannan”. Inji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai