APC Ga Fayose: Ba Mu Bukatar Mutum Irinka A Cikinmu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

APC Ga Fayose: Ba Mu Bukatar Mutum Irinka A Cikinmu

Published

on


A shekaran jiya ne jam’iyyar APC reshen Jihar Ekiti ta bayyana cewar bata shirya karbar  tsohon gwamnan jihar Mista Ayo Fayose zuwa cikin ta ba.

Ranar Litinin dai Fayose ya bayyana niyyar sa ta barin jam’iyyar PDP, lokacin da yake fadar albarkacin bakin cikin shi na yadda aka aiwatar zaben fidda gwani na ‘yan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Paul Omotoso, shugabannin dukkan mazabun kansiloli na Karamar hukumar Irepodun/ Ifelodun ta mazabun Kansilan 13 na Ado- Ekiti, inda gwamnan ya zauna, yake kuma tafiyar da harkokin sa, da cewar ya manta da maganar barin jam’iyyar PDP da kuma niyyar komawa jam’iyyar APC. Har sai lokacin dab ya wanke kan shi akan laifuka masu yawa da ake zargin shi da aikatawa.

A cikin bayanan data fitar wanda sakataren yada labaranta Honorabul Ade Ajayi yaba tsohon gwamnan mai baring ado da cewa ya kammala matsalolin  shi da suka shafi kotu, da suka hada da laifuka masu nauyi, kafin ya yi tunanin shiga jam’iyyar APC.

Yab Kara bayyana cewar “ Muna son mu  nuna ma duniya cewar ‘jam’iyyar APC ba zata kasance wata mabuya bace ga adanda suka aikata laifi,  ba zamu taba ba masu irin wannan halin  ba dama ba, bazamu taba amincewa da masu irin wannan halin zua APC ba, shi yasa muke ba Fayose shawarar da cewar ya je wani wurin inda yake siyasar shi  ta rashin kunya da kuma cin mutuncin.

Za dai a ci gaba da shariar zargin da ake yi ma Fayose shari’a akan laifukan da ake zargin ya aikata, ranar 4 gawatan Nuwamba na wannan shekarar, wato laifukan da ake zargin da aikatwa a shekarar 2005 wadanda suka hada da  badaKalarb gonar kiwon kaji ta shekarar 2005, idan kuma ba hakan ba, to ya daura  a zuciyar shi cewar ya manta da duk wata sha’awar da yake yi ta komowa  cikinta:’

Omotaso ya bayyana ma  Fayose cewar “APC ita jam’iyyar siyasa ce wadda take da wasu shika shikan riKe gaskiya da amana, yin abu babu wata Kunbiya Kunbiya, ga kuma ladabi da biyayya, sadaukar da kai ga al’amarin da zai tabbar da ana aiwatar da gwamnati yadda  ya kamata  kamar yadda shi shi  ba wai wasu al’amura shi Fayose ya mallaka ba. da kuma sanin  yadda al’amuran suka tafi a kwanakin baya.”

Ya Kara jaddada cewar “ Shekarun da suka wuce Fayose ya zagi Shugaban Kasa, da yi ma shi wasu abubuwan, adanda suke nuna ashe lalle bai ganin Kimar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne shugaban mu kuma shugaban jam’iyya, da kuma  babban kwamanda na askarawan Nijeriya.

“Fayose yana son ya dawo ya shiga jam’iyyar saboda ya lalata ta, saboda ya tabbatar da cewar  Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bai samu  tsallakewa zuwa zango na biyu be, ko kuma karo na biyu, saboda haka ba zau bari ba ita jam’iyyar ta lalata ce ba.

Omotoso wanda y ace ba yadda za a yi a  amince ma Fayose ya dawo jam’iyyar APC ba, saboda haka y aba shi gwamnan shawarar cewar daya duba zuwa wani wuri watakila ya samu jam’iyyar da zai koma, wadda kuma zai iya lalatawa, bayan da ya bata jam’iyyun siyasa uku na Kasa, bayan da yaga ba yadda zai yin ya yi iko dasu.

“Fayose yay a fadi abubuwa da yawa lokutan da suka wuce wadanda shi yake tsammanin zasu bata jam’iyyar APC, ya lalata jam’iyyar labour party (LP) All Nigerian People’s Party  (ANPP) akwai ma lokacin daya bata jam’iyyar PDP, kafin a kai ga yanayin da ikta jam’iyyar PDP take a jihar Ekiti.

“APC  tana neman wadanda zasu gina tane amma ba masu lalatata ba a indab take da mutunci, ba zamu taba amincewa da shi wannan mai barna ba, a cikin wannan babbar jam’iyya tamu APC. Muna kuma Kara tuna ma shi Fayose ya tafi wanin wurin  ya iya samun jam’iyya da kuma mutanen da suka dace dashi, inda zai samu dama ya ci gaba da yin aikin nashi daya saba da yi”.

Ya ja kunnen shugabannin ward ward wato mazabiun kansila kansila inda shi Fayose yake zaune, yani harkokin kasuwancin shi, da kada su kuskure su amince da shi zuwa jam’iyyar APC.

Ya ci gaba da cewar “Jam’iyyarmu ba wani wuri bane inda marasa gaskiya zasu zo su riKa samaun mafaka ba, kuma masu bata jam’iyya, ya kamata su je jam’iyyun da suka dace dasu.

“ Don haka shi yasa muke jan kunnen shugabannin ward- ward inda shi Fayose yake zama da kuma yin harkokin shi, kada su yarda su shigo da shi jam’iyyar APC.

“Donn haka muke kira da shugabannin jam’iyyar APC musamman na ward ward ba wanda zai magana da Fayose, har sai shugaban jam’iyyar na ward ya samu amincewar shugaban jam’iyyarb na jiha.”

Advertisement
Click to comment

labarai