Ba Na Jin Dadin Zaman Barcelona -Vidal — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ba Na Jin Dadin Zaman Barcelona -Vidal

Published

on


Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Arturo Vidal, dan kasar Chile, ya bayyana rashin jin dadinsa a kungiyar bisa rashin buga wasa dayake a kungiyar tun bayan komawarsa daga Bayern Munchen

Bidal, mai shekara 31 a duniya yakoma Barcelona ne daga Munich akan kudi fam miliyan 26 sannan ya saka kwantaragin shekara uku sai dai kawo yanzu wasa biyu aka fara dashi a a kungiyar.

Sai dai Bidal wanda a yanzu yake kasar Amurka domin buga wasa tsakanin kasarsa ta haihuwa Chile da Peru, ya bayyana cewa sunyi Magana da kociyan kungiyar ta Barcelona akan abinda yake damunsa.

“Tabbas ba na jin dadin abinda yake faruwa na rashin buga wasa saboda har yanzu ban buga wasa cikakke ba na minti 90 wanda kuma wannan ba abu bane wanda zan tsaya ina zuba ido saboda har yanzu da kwarina” in ji Bidal

Ya ci gaba da cewa “Bazan taba zama nai farin ciki ba idan bana buga wasa saboda ni dan wasa ne mai son buga wasa kuma kowa yasan da haka kuma na lashe kofuna da dama a duniya sannan kuma inason ci gaba da lashe wa a Barcelona”

A karshe yace lafiyarsa kalau bashi da ciwo gaba daya amma kuma zaici gaba da hakuri saboda akwai wasanni anan gaba masu amfani kuma yasan cewa zaiyi amfani idan lokaci yayi.

Advertisement
Click to comment

labarai