Bayern Munchen Na Son Zidane — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Bayern Munchen Na Son Zidane

Published

on


Rahotanni daga kasar Jamus sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen dake kasar ta fara tunanin zawarcin tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, wanda Manchester United aka ce tana nema.

Zidane ya lashe kofin zakarun turai guda uku a jere a Real Madrid cikin shekara biyu da rabi da gasar Laliga guda daya sai dai ya yi ritaya daga koyar da kungiyar a watan Mayun daya gabata saboda wasu dalilai.

A kwanakin baya dai aka dinga danganta Zidane da komawa Manchester United sakamakon rashin kokarin kociyan kungiyar Jose Mourinho sai dai yanzu itama Bayern Munchen tashiga neman tsohon dan wasan na Faransa.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen dai bata fara buga kakar wasa da kafar dama ba bayan da a halin yanzu take mataki na biyu maki hudu tsakaninta da wadda take mataki na daya wato Dortmund

Rashin nasarar da kungiyar tayi a hannun kungiyar Borussia Manchengladbach a satin daya gabata daci 3-1 da kuma canjaras da kungiyar Ajad a gasar zakarun turai shine yasa ake ganin kungiyar za ta iya rabuwa da sabon kociyan nata.

Bayern Munchen dai ta dauki Nico Kobac, wanda tsohon dan wasanta ne a farkon kakar wasa sai dai kociyan bai fara buga wasanni da kafar dama ba kuma tuni kungiyar ta fara tunanin canja shi domin samun canji a sakamakon wasanni.

Advertisement
Click to comment

labarai