CBN Za Ta Rage Kudin Da MTN Ke Neman Kai Wa Afrika Ta Kudu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

CBN Za Ta Rage Kudin Da MTN Ke Neman Kai Wa Afrika Ta Kudu

Published

on


Mai yuwa Bankin CBN zai rage yawan kudin data umarci kamfanin sadarwa na MTN take son fitar dasu zuwa kasar Afirka ta Kudu.

Gwamnan bankin Godwin Emefiele wanda ya sanar da hakan a ranar Lahadin da ta wuce ya ce, a lokacin hirarsa da manema labarai a Birtaniya.

Emefiele ya ce, sabon kudin zai bayar da dama ga kamfanin sadarwar yadda zai taimaka wajen rage yawan fadin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito  Emefiele a lokacin da ya kai ziryara  Birtaniya yana cewa , “Bana tunanin hakan zai taimaka wajen yadda za’a kai dala biliyan takwas, inda ake sa ran za’a shawo kan maganar  a cikin sauki.

Abewar sa, “Ina mai imani cewar, adadin zai ragu, inda ake ganin ko zai sauka baki daya amma maganar gaskiya ba zan iya fada ba a wannan lokacin.”

Emefiele ya ci gaba da cewa, CBN ya karbi kundi kimanin guda biyu a satattukan da suka wuce daga gun MTN kuma masu bayar da bashi su hudu suma suna cikin maganar da suka hadada, cibiyar Standard Chartered, bankin  Stanbic IBTC, bankin Citi da kuma bankin  Diamond kuma ana kan tattaunawa da wadanda abin ya shafa.

A cewar sa, CBN zai yi nazari akan wannan yadda zai kai zuwa matsayi na, ya kara da cewa, yana sa ran zai samu sakamako nan da satutttuka masu zuwa.

Ya yi nuni da cewar, bangarorin biyu suna kotu a kan rikicin hada-hadar bayan da CBN ya shigar da yin jayayya a ranar juma’ar data gabata kamar yadda MTN ya bukata bayan da ya bukaci bankin a kan cewar an tilasta masa ya dawo da kudaden.

Gwamnan bankin ya kara da cewa,CBN ya bukaci kamfanin dake da zama a Johannesburg ya biya kashi 15 bisa dari na kudin sa na ruwa na shakara ga har sai kotun ta yanke hukuncin ta da kuma biyan kashi 10 bisa dari daga cikin gundarin kudin

Emefiele ya ce, rikicin MTN CBN baya kallon maganar hada-hadar data hada da wasu kamfanonin da suke gudanar da ayyukan su a kasar nan.

A cewar sa,“muna girmama ko wanne kamfani kuma CBN zai ci gaba da shiga tsakani a kan musayar kudade na kasar waje a kasuwar shinku.

Ya jadda da cewar, ci gaba da ake yi a kan matsin lamba a kan kudin kasar nan za a ci gaba da yin hakan.

Rikicin a kan maido da dala biliyan takwas ya samo asali ne a lokacin da CBN ya zargi MTN wajen samar da sheda ba’a bisa ka’ida ba wajen fitar da kudin daga kasar nan a shekarar  2007,inda  MTN ya karyata maganar rikicin.

CBN ya ce, bankunan  da MTN yake yin ajiya sun gaza wajen bincika rukunonin kamfanin tabbatar  na cewar ko kamfanin ya cika dukkan sharuddan da suka dace na kasar nan na musayar kudaden ksar waje.

A saboda hakan ne ya sanya CBN ya kakaba jimlar Naira Biliyan 5.87 a kan bankunan a bisa zargin tura riba ta hanyar yin amfani da shedar da bata dace ba da sunan MTN dake Nijeriya daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2015.

Advertisement
Click to comment

labarai