Dan Majalisa Ya Horas Da Manoman Shinkafa 50 A Sakkwato — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Dan Majalisa Ya Horas Da Manoman Shinkafa 50 A Sakkwato

Published

on


Dan Majalisar Wakilai Hon. Isa Salihu Bashir Kalanjeni ya horas da manoman shinkafa 50 dabarun yadda ake noman shinkafa na zamani, yabanyarta da sarrafa ta a mazabar sa da ke a Tangaza/Gudu da ke a Jihar Sakkwato.

Manema labarai sun ruwaito cewar an gudanar da horon ne na kwanaki biyu tare da hadin guiwar Cibiyar Bincike da Adana Amfanin Gona ta Kasa (NSPRI)

Malam Musa Gidan-Madi daya daga cikin wadanda suka jagoranci gudanar da taron ya bayyana cewar an zabo mahalarta taron ne daga dukkanin mazabu na mazabar Tarayya ta Tangaza/Gudu ya kuma ce mafi yawan al’ummar yankin manoma ne da ke samun riba a kasuwanci musamman saboda suna da albarkar kasar noma mai kyau.

“An horas da mahalartan domin su ma su koyar da sauran al’umma, misali sun amfana da yadda ake mayar da shinkafa gari, daga gari kuma a na iya yin tuwo da ita, an ilmantar da su irin nau’in kasar da ta dace da noman shinkafa kala daban-daban da yadda ake yabanyarta irin yabanya ta zamani.” Ya bayyana.

Gidan-Madi ya ce an horas da mahalartan cewar noman shinkafa kala-kala ne domin akwai shinkafar da ake mayarwa gari a kuma yi masa da ita da kuma shinkafar tuwo da yadda za a yi biredi da shinkafa ba tare da an dogara da fulawa ba.

Da yake jawabi  Dakta Sam O. Okunade Shugaban Sashen Binciken Amfanin Gona na Cibiyar ya bayyana cewar horon ya bada kaimi ne kan yadda ake sarrafa sninkafa a nau’uka daban-daban da yadda ake kyakkyawar shuka da kuma yadda ake ingantacciyar yabanya mai kyau.

A zantawarsa da manema labarai, Hon. Isa Kalanjeni ya bayyana cewar makasudin bayar da horon a mazabarsa shine mafi yawa kauye shinkafa dafawa kawai ake yi, ko a yi mata wasa-wasa a sa mai da yaji, to amma akwai abubuwa sama da 20 da ake yi da shinkafa.

Dan Majalisar wanda ya sake samun tikitin takara karo na hudu a PDP ya ce “A na yin biredi da shinkafa, a na yin cin-cin, donot, meat pie, da sauran kayan soye-soye irin wadanda ake yi da fulawa. Idan aka sarrafa ta idan ba an sanar da kai ba ba za ka taba gane cewa shinkafa ba ce, wato kamar magani ne a gonar yaro amma bai sani ba ya sare.” In ji shi.

Ya ce a da cin shinkafa kawai ake yi ko a yi tuwo da ita amma yanzu zamani ya sa an san amfanin ta don haka ya kamata a dage da noma.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da horon Malam Musa Garba da Aliyu Balle sun bayyana horon a matsayin wanda ya dace wanda kuma zai amfani al’umma tare da karfafa noman shinkafa da sarrafa ta a Jihar.

Advertisement
Click to comment

labarai