Fidda Gwani A Zamfara: Takaddama Ta Kaure Tsakanin INEC Da APC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Fidda Gwani A Zamfara: Takaddama Ta Kaure Tsakanin INEC Da APC

Published

on


  • Babu ’Yan Takarar APC Daga Zamfara A Zaben 2019 -INEC
  • Ba Haka Batun Yake Ba, Muna Da Dan Takara -Oshiomhole
  • Babu Wani Zaman Sulhu Da Aka Yi –Sanata Marafa

Takaddama ta kaure tsakanin Hukumar INEC da Jam’iyyar APC kan ‘yan takarar Jam’iyyar APC da za su shiga sahun fafatawa a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Wanna ta sa Shugaban Jam’iyyar APc, Adams Oshiomhole ya mayarwa da Hukumar INEC martani da cewa Jam’iyyar tasu tana da ‘yan takararta, domin kuwa an cimma matsaya ta sulhu a tsakanin ‘yan takarar a ranar 7 ga watan Oktoba 2018 a Otal din ‘King’ dake Gusau.

Sai dai a wata sabuwa kuma, Daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar APC a Zamfara, Sanata Kabir Garba Marafa ya sanar da LEADERSHIP A Yau cewa, Karya ne babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara.

Tun farko dai a jiya Hukumar ta INEC ta rubuta wasiKa zuwa ga Oshiomhole, inda ta bayyana cewa, jam’iyyyar APC ba ta da hurumin gabatar da ‘yan takara matsayin Gwamna da majalisar tarayya da majalisar dokokin jihar na jihar Zamfara gaba daya.

A wasiKar wanda mai riKe da muKamin sakataren hukumar ya sanya wa hannu, ya ce,

“Ku lura da tsarin jadawalin zabe da hukumar da fito da shi na tsare tsaren harkokin zaben 2019 wanda aka raba wa jam’iyyun siyasa a watan Janairu na 2018. A cikin jadawalin an shirya gabatar da zaben fidda gwani a tsakanin ranar 18 ga wata Agusta zuwa ranar 7 ga watan Oktiba 2018.

“Amma bayanai dake fitowa daga jihar Zamfara ya nuna cewa, duk da mutanenmu na nan a jjihar don ganin abin da zai faru babu wani zaben fidda gwanin da ya gudana a jihar gaba daya. “A saboda haka kuma mun lura da tanade tanaden dake a sashin dokar zabe na shekara 2010 sashi na  87 da 31, don haka bama sauraron wani suna na ‘yan takara daga jihar Zamfara na jam’iyyar ku ta APC ba za ta gabatar da ‘yan takara ba a zaben dake tafe na 2019.

Don Karin fahintar daku muna nufin cewa, jam’iyyar APC ba za ta gabatar da ‘yan takara a kan muKaman Gwamna da Majalisar Kasa da majalisar dokoki na jiha a zaben da za a gudanar na 2019”.

Haka kuma LEADERSHIP A Yau a kwanakin baya ta ruwaito cewa a ranar 5 ga watan Oktoba ne kwamitin zartasawa na jam’iyyar ta rusa shugabannin gudanarwa na jam’iyya a jihar Zamnfara a dukkan mataki bayan da suka gudanar da zaben fidda gwanin da aka yi taKaddama a kai a ranar Laraba 3 ga watan Oktoba da kuma ranar Alhamis 4 ga watan Oktoba.

Sakataren jami’yyar, Mista Yekini Nabena, ya ce, wannan shawarar na nuna cewa, an rushe dukkan shugabannin jam’iyyar na dukkan matakai a jihar kenan. Shugabannin da aka rusa sun sanar da gudanar da zaben fidda gwanin da suka ayyana dan takarar gwamnan na bangaren Gwamna yYari, Alhaji Mukhtar Shehu Idris a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar takarar gwamna sannan kuma shin kanshi Yari ya lashe zaben kujerar takarar majalisar dattijai na yankin Zamfara ta Yamma, shugabanin jam’iyyar na Kasa suka haramta sakamako zaben gaba daya.

Daga nan ne shugabannin jam’iyyar suka Kaddamar da kwamiti don gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar gaba daya a ranar Asabar 6 ga watab Oktoba zuwa Lahadi 7 ga watan Oktoba. Amma kwamitin ta kasa gudanar da zaben saboda barazanar da gwamna Yari ya yi n a gudanar da zanga zanga in har suka gudanar da zaben.

Advertisement
Click to comment

labarai