Gwamna Masari Ya wanke Kansa Dangane Da Zaben Fidda Gwanin APC A Katsina — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Gwamna Masari Ya wanke Kansa Dangane Da Zaben Fidda Gwanin APC A Katsina

Published

on


Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa an jawo hankalinta cewa wasu jami’an jam’iyyar APC da shugabannin kwamitocin riko suna zagayawa don shedama masu jefa kuri’a cewa wai gwamna ya na da ‘yan takara.

Kamar yadda wata sanarwar tace wai ana umurta masu jefa kuri’a din su zabisu wadancan wadanda ake cewa yan takarar gwamnan ne a zabukan fidda gwani.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai taimakama gwamna na musamman akan kafafen yada labarai Abdu Labaran Malumfashi ya bayyana cewa babu lokacin da gwamnan ya furta hakan.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar Katsina ba zata yi wani abu ba da zai sabawa kundin tsarin mulki na jam’iyyar APC ba, wanda ya nuna kurun yadda za’a gudanar da aikace-aikace jam’iyya day a hada da zaben fidda gwani.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ba ta taba yin katsalandan ba cikin al’amurran, tana bari ne ayi abubuwa yadda ya kamata.

Sanarwar ta kara jaddada cewa masu nemana zabe su a mukaman siyasa musamman wadanda suke ganin ba zasu samu nasarar ba zasu iya yin komai domin ganin cewa sun haddasa matsala kafin a fara zaben.

Dangane da hakan ne, sanarwar ta shawarci yan takara da magoya bayanansu su bi sannu sannu da masu neman dama wanda halayensu shi ne idan basu samu abunda suke so ba to kowa ma ya rasa.

Bugu da kari kuma, an shawarci masu ruwa da tsaki da suji watsi da jami’an jam’iyyar dana gwamnati komin matsayinsu wanda suke gaya masu wani abu da ya sabawa kundin hakanan.

Kuma an bayyana sakamakon zabe na fidda gwani wakillai na Katsina ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC.

Da yake bayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin zaben, Dr. Haruna Yarima from jami’ar Ahmadu Bello Zaria ya bayyana cewa Salisu Iro Isansi shi ne ya samu nasara a inda ya samu kuri’u 126.

Ya bayyana cewa Sani Aliyu Danlami ya zo na biyu da kuri’u 76, Saddik Ayuba ya zo na ukku da kuri’u 55, Musa Sada kuru’u 40, sannan kuma Isa Barda ya samu kuri’u 43 a inda kuri’u sha ukku suka lalace.

Dr. Haruna Yrima ya bayyana cewa jimillar kuri’u 358 aka kada a lokacin zaben fidda gwani.

Wakilinmu wanda ya duba yadda aka kirga kuri’un da kuma bayyana sakamakon zaben, ya bayyana cewa wakillan yan takarar suna wurin da ake kirga kuri’un.

Advertisement
Click to comment

labarai